ABIN TAUSAYI: Yadda sakacin mahukuntan ya jawo aka yankewa Dalibar makaranta hannu a Jigawa
Daga Saratu G Abdul
Wannan wata baiwar Allah ce, Safiya Abbas yar shekara 15 da ta fito daga yankin Jahun wacce ke karatu a makarantar Kwana ta mata dake Miga wato Science Secondary School Miga.
Rahotanni sun ce a kwanakin baya Safiya ta samu mummunan yanka a hannunta wanda ya shiga sosai, a inda Matron din Hostel dinsu ta rasa yadda zata yi domin wai Principal dinsu wacce gidanta ke cikin makarantar ta bada umarni cewa kome zai faru a cikin makaranta kada wanda yayi gangancin zuwa gidanta ya fada mata domin ka’idarta shine indai ta shiga gida babu abinda zai fito da ita sai lokacin da taga damar fitowa.
Wata da ta shaida abun, Saratu G Abdul ta wallafa cewa ganin Safiya tana ta zubar da jini kuma ga tsananin ciwo da take fama dashi yasa Matron din ta yi kokarin bata taimakon gaggawa wajen yin amfani da kashin bera da nikakken wake ta zuba mata da daure mata hannun.
To kasancewar anyi amfani da gurbatattun abubuwa a ciwon ya sanya ciwon ya harbu da cututtuka gashi kuma yankan ya shiga sosai. A haka yarinya tai ta wahala har sai bayan kwana biyu lokacin da Hakima Principal ta ga damar fitowa daga gidanta.
Ganin yadda ciwon ya lalace sai aka kaita Asibitin Jahun inda aka rika yi mata dressing amma kuma kasancewar babu wata kyakyawar kula yasa hannun yaci gaba da lalacewa.
Daga karshe dai iyayen Yarinya suka ga babu Sarki sai Allah suka dauketa zuwa babban Asibitin kwararru na Rasheed Shekoni dake Dutse inda bayan an duba anyi gwaje gwaje aka tabbatar masu da cewa yatsan ya lalace dole ne a yanke shi tare da diban nama daga wani sassan jikinta domin ayi mata ciko a wani bangaren.
Hakan kuwa akayi aka yanke akayi mata ciko kamar yadda suka ce wanda iyayen yarinyar duk suka dauki nauyin komai da komai na zaman asibiti da maganin da kuma aikin da akai mata.
Yarinya dai ta cutu ba karamar cutuwa ba domin kuwa an nakasata to amma wanne mataki aka dauka ko kuma za’a dauka don ganin cewa an biwa wannan yarinya hakkinta?
Me Gwamnatin Jigawa zatayi akai?
Me Ma’aikatar Ilmi ta Jigawa zatayi akai?
Me sauran qungiyoyin sa kai zasu ce?
Mu taimaka wajen yada wannan labari har yakai inda ya kamata ya kai.
Share! Share!! Share!!!
Add Comment