-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Yadda Sakacin Gwamnatin APC Da Buhari Ya Jawo Asarar Sama Da Ayyuka Milyan 12 – Atiku


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yadda sakacin gwamnatin APC da Buhari ya jawo asarar sama da ayyuka milyan 12 – Atiku

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci daukacin al’ummar Nigeria da su sauke shugaban kasa mai ci a yanzu Muhanmadu Buhari ta hanyar kin zabarsa bisa gazawarsa na cika alkawuran da ya dauk a yakin zaben 2015.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 656

- Advertisement -

Atiku ya bayyana hakan ne a wajen taron gangamin yakin zabensa na shiyya da aka gudanar a babban filin taro na Mapo, da ke Ibadan.

A wajen gangamin yakin zaben, akwai jiga jigan jam’iyyar PDP da suka halarta, irinsu shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinla; tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel; Sanata Ben Bruce, da kuma tsohon ministan wasanni da muhimman ayyuka, Farfesa Taoheed Adedoja, da dai sauransu.

Atiku ya ce: “A 2015, wasu makaryata, marasa imani suka zo wannan waje don yaudararmu kuma muka basu kuri’unmu. Sai dai mun gano cewa sun kasa cika alkawuran da suka daukarwa al’ummar Nigeria. A tarihin kasar nan, ba a taba samun mulki mai cike da adalci, walwala, zaman lafiya da bunkasar ilimi kamar a lokacin jam’iyyar PDP ba.” Shi (Buhari) ya yi mana alkawarin samar da ayyukan yi. Amma a maimakon hakan, an rasa sama da guraben ayyuka milyan 12. Sun yi alkwarin kawar da talauci amma kasarmu ce shelkwatar kasashe masu fama da ukubar talauci. Shin irin wannan gwamnatin ce kuke so taci gaba da mulkarku? Idan har aka bani dama,zamu dawo da martabar wannan kasar tamu.”

“Kowa ya san cewa ina jagorantar tawagar kwararru kan tattalin arziki a kasar nan. Idan har aka sake bani sama,zan hada tawagar mutane mafi kwarewa da zasu dawo da martabar tattalin arziki a kasar. Kowa ya san shiyyar Kudu maso Yamma da kaurin suna wajen ilimi, idan aka bani dama, zan tabbata na dawo da martabar ilimi a wannan shiyya.” a cewar Atiku

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: