Labarai

Yadda Na Taimaka Wajen Jefa Nijeriya Cikin Yunwa Da Talauci

Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa shi da sauran jiga-jigan jam’iyyarsa ta APC ne suka jefa Nijeriya cikin halin yunwa da bakin talaucin da kasar ke ciki a yau.

Melaye da ya yi kaurin suna wajen jaye-jayen rigingimu iri daban-daban ya bayyana hakan ne a matsayinsa na daya daga cikin wadanda aka zaba su yi alkalancin wata muhawara da OSASU SHOW ta shirya a Abuja, mai taken: “The New Economy and its Impact on less Privilege” wato (Sabon tsarin tattalin arziki da tasirinsa akan masu karamin karfi) da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.

 

Melaye ya ce “Yadda ‘yan siyasa ke gudanar da siyasa shi ne sanadiyyar fadawarmu halin kaka-ni-ka-yi da kasar ta shiga.
Su kuma yunwa da talauci basu da jam’iyya”

“In ka fadi gaskiya, ka kira ajalinka, haka kuma in ka yi karya, nan ma dai ka kira ajalinka.
Saboda haka na zabi na fadi gaskiya, gaskiyar ta zama ajalina.

A gaskiyar zance, bayan tsarin mulki irin na soja, siyasa itace sababin talauci da yunwa a Nijeriya,” inji Melaye

“Abin kaico, shi ne, shugabanni a Nijeriya, har da ni a ciki, mun gaza kai kasar nan ga tudun muntsira
Kuma mun haifar da illa ga karni na gaba na kasar nan.
Dalilin da ya sa muke a wannan hali shi ne
Saboda akwai wawakeken gibi tsakanin shugabanni da wadanda suke mulka”

“Sam babu yarda tsakanin shugabanni da talakawa.

Wannan ko shakka babu babbar matsala ce”
“Kuma da zarar an samu irin wannan rashin aminci tsakanin masu mulki da talakawa, tasirinsa sai koma kan tattalin arziki ga sauran al’amuranmu na rayuwa”

Melaye ya ci gaba da cewa matsalolin da ke addabar Nijeriya ba su da jam’iyya ba su da mazaba a saboda haka dukkanmu ya kamata mu hada karfi da karfe wajen yakarsu”
“Yunwa da talauci basu da jam’iyya, basu da addini, basu da mazaba.

A saboda haka ba daidai bane a kira mutane wajen tattauna wata muhawara akan matsalar yunwa da talauci a matsayin ‘yan PDP da APC, saboda talakan APC da na PDP kasuwa daya suke zuwa,” inji Melaye.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.