Kannywood

Yadda na soma zama darakta – mawaƙiyar Kannywood Farida Ajebo

advertisement

FARIDA Usman, wadda aka fi sani da Farida Ajebo, ba sabuwar fuska ba ce a Kannywood, domin kuwa ta daɗe ta na bada gudunmawa a masana’antar a fannoni da dama. Ban da waƙa, Farida jaruma ce, mai shiryawa ce, kuma darakta ce. Ana iya cewa ta biyo sahun tsohuwar jaruma Muhibbat Abdulsalam kenan.

Farida dai santaleliyar yarinya ce mai ladabi da biyayya ga kowa a industiri, har ma da wajen ta, domin duk inda za ka ji an ambaci sunan ta sai ka ji an yabi kyawawan halayen ta.

Mujallar Fim ta tattauna da ita game da rayuwar ta, yadda aka yi ta fara waƙa, nasarori da ƙalubalen da ta fuskanta a masana’antar ta fimafinan Hausa, yadda ta zama jaruma, mai shiryawa, sannan kuma ta fara rikiɗa zuwa mai bada umarni, waye ubangidan ta da dai sauran su.

Ajebo ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wurin amsa dukkan tambayoyin da wakilin mu ya yi mata, kamar haka:

FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin ki a taƙaice.

FARIDA AJEBO: Assalamu alaikum. Ni dai suna na Farida Usman, amma an fi sani na da Farida Ajeboter, saboda inkiyar ta fi ƙarfi. An haife ni a Jihar Sokoto, amma aiki ne ya kai baban mu can. Daga nan kuma mu ka dawo garin Abuja. A can mu ka girma. Bayan rasuwar kakan mu ne mu ka dawo Kaduna, har na zama cikakkiyar ‘yar Kaduna ta dindindin.

Na yi karatun firamare na a ‘Jibril Memorial’, na kuma yi sakandire na a ‘Karu Secondry School’, sannan na je ‘School of Health’, Maƙarfi, inda na yi ND na da HND a can.

FIM: A ina sunan Ajeboter ya samo asali?

FARIDA AJEBO: Wannan sunan na Ajeboter ya samo asali ne daga wurin mahaifi na. Dalili kuwa, lokacin ƙanwa ta ta na ‘Police Secondary School’ ana kiran ta da Skelegaga, sai ake tambayar ta menene Skelegaga. Sai ta ke cewa ita dai sunan da ta ke so kenan. Sai aka ce mata, “Wato ma Skeleton kenan, kin yarda?” Sai ta ce e, ta yarda. Sai baban mu ya ce, “Ai ‘ya ta ce Ajebo!” To tun daga lokacin ya kasance ana kira na da sunan, har ya bi gari, kowa Ajebo; wasu ma ba su san sunan Faridan ba, sai Ajeboter. Ka ji yadda aka yi na samu sunan kenan.

FIM: Ke wace ƙabila ce?

FARIDA AJEBO: Ni Bafulatana ce daga Jihar Adamawa.

FIM: Ya aka yi ki ka fara waƙa?

FARIDA AJEBO: Wow! Ina son waƙa. Gaskiya ina son waƙa, saboda tun ina sakandire ina ‘Hausa Club’, a lokacin mu ne mu ke rera waƙa. In za a yi taro, za mu haɗu a ce a yi wannan waƙar ko kuma a yi waƙa kaza ko waƙa kaza. A haka dai mu ka fara waƙa, har ya kasance mun gama makaranta. Na zo na haɗu da wasu, su ka ce min ai su su na da situdiyon waƙa. Sai na ce, “Situdiyo fa! Ai ni ma ina so in yi waƙa; mu je!”

Mu ka je. Aka ce min, “Za ki iya kuwa?” Na ce, “Zan iya mana.” Ana buɗe min sai na rera waƙar nan. Sai na ce, “Ashe zan iya waƙa!” Daga nan ga shi har abin ya girma.

FIM: Da wace waƙa ki ka fara?

FARIDA AJEBO: Gaskiya ni ba zan iya tuna sunan waƙar da na fara yi ba. Amma waƙar dai ta siyasa ce.

FIM: Daga lokacin da ki ka fara waƙa zuwa yanzu, aƙalla kin yi waƙoƙi sun kai nawa?

FARIDA AJEBO: Cab! Gaskiya ban sani ba. Amma a ƙiyasi zan iya cewa za su kai hamsin ko ɗari. Nawa na kai na kuma za su kai ashirin ko fiye da haka ma.

FIM: Ki faɗa mana wasu daga cikin waƙoƙin ki.

FARIDA AJEBO: Akwai waƙar ‘Kafin Aure’, ‘Matan Gida’, ‘In Dai Da Tunani’, ‘Mai Kunya’, ‘Da So Mu Ka Saba’, ‘Ki So Ni’, duk waƙoƙi na ne; akwai bidiyon su, da sauran waƙoƙi na.

FIM: Wanene ubangidan ki?

FARIDA AJEBO: Ina da ubangida, gaskiya. Kuma ba wani ba ne illa Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa).

FIM: Bayan shi babu wani?

FARIDA AJEBO: Akwai abokan sana’ar waƙa, amma wasu sun fi so a kira su da ubangida, kamar El-Mu’az Birniwa, don shi ma zan iya kiran shi da ubangida, domin na kan samu abubuwan alheri da sauran su.

FIM: Ke ki ke rubuta waƙa da kan ki ko rubuta maki ake yi? Domin yawancin matan da ke waƙa rubuta masu ake yi. Ya ki ke naki tsarin?

FARIDA AJEBO: Gaskiya ni na ke rubuta waƙoƙi na, amma yawancin lokuta idan na rubuta ya rage kamar baiti ɗaya kuma ya gagare ni, na kan je na samu Jibril Jalatu in ce masa ina rubuta waƙa amma na kakare, ya za a yi? Sai ya ce min, “Ki bari mu haɗu” ko kuma, “Zo ki same ni a situdiyo.” Daga nan kawai sai ka ga abu ya cika cif-cif.

FIM: A wane situdiyo ki ka fi jin daɗin yin aiki?

FARIDA AJEBO: A Hannun Dama, situdiyon Ala, wurin Auwal, saboda shi ne zai gyara min waƙa ta ka ji ta ta fita fes.

FIM: Da wane mawaƙi ki ka fi jin daɗin yin waƙa?

FARIDA AJEBO: Na fi jin daɗin yin waƙa da Jibril Jalatu sosai gaskiya, saboda waƙa ta da shi ta fi tafiya.

FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu a harkar waƙa?

FARIDA AJEBO: Alhamdu lillahi! Na samu nasarori da dama, saboda wasu lokutan za ka samu kyautar kuɗaɗe, ko a ce maka an biya maka abu kaza, in za ka je ne ka je, in kuma kuɗin ka za ka karɓa ka karɓi kuɗin ka. Amma dai kyautar kuɗi, ka na zaune wanda ma ba ka taɓa tsammani ba sai ya kira ka ya yi maka kyauta.

Farida Usman (Ajeboter): “Ina da ubangida … Alan Waƙa”

FIM: A wace irin waƙa ki ka fi ƙwarewa? Wasu sun fi ƙwarewa a waƙar siyasa, wasu ta soyayya, wasu ta faɗakarwa, wasu ta jinjina.

FARIDA AJEBO: Gaskiya na fi ƙwarewa a waƙar faɗakarwa sosai fiye da ta soyayya, duk da dai ina yin ta soyayyar ita ma sosai.

FIM: Wace waƙar ki ce ta yi fice?

FARIDA AJEBO: Waƙar ‘Matan Gida’ da ‘Kafin Aure’ su ne su ka yi fice sosai a waƙoƙi na na faɗakarwa.

FIM: Waɗanne irin saƙonni ki ka aika a cikin waƙoƙin?

FARIDA AJEBO: Kamar waƙar ‘Matan Gida’, za ka ga a kan zaman cikin gida ne, gidan haya hakan nan. Za ka ga wata ta raina mijin ta, ta raina uwar mijin ta, ta raina mahaifin sa, kowa nashi abin rainawa ne, sai shi ɗin kawai da ta ke gani, kuma shi ɗin ma bai sha ba a wurin ta. Amma wata a cikin gidan ko kuɗin cefane ba a ba ta, amma ta na haƙuri da duk irin musguna mata da za a yi; dangin miji su zo su yi mata cin mutunci da sauran su, amma ba ta ɗaukar waɗannan abubuwan, za ta yi haƙuri saboda mijin ta da ta ke so. Saboda irin waɗannan abubuwan na yi waƙar ‘Matan Gida’.

Ita kuma waƙar ‘Kafin Aure’, a kan ma’aurata ne. Za ka ga wasu kafin su yi aure za ka ga ana soyayya sosai a waje kamar ba za a rabu ba, babu wulaƙanci. Amma daga an yi auren nan mace ta samu ciki, wasu da ma burin su kenan su ga matar su ta samu ciki, ta na samun cikin nan ta zama abar wulaƙantawa a wurin su. Ko me za ta yi ba za ta burge su ba, sun gwammace su je wurin wata ko su ɗauko wata su kawo ta gidan don su wulaƙanta matar su a idon duniya. To, saboda irin wannan abin ne na yi waƙar ‘Kafin Aure’.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button