-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Yadda Jaruma Hauwa Maina Ta Rasu


2 2,987

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A ranar Larabar , 2 ga Mayu, 2018, fitacciyar jarumar finafinan Hausan nan, Hajiya Hauwa Maina, ta riga mu gidan gaskiya. Ta rasu ne ta na da shekaru 48 da haihuwa a asibitin Malam Aminu Kano da ke birnin Kano bayan ta sha jinya.

Majiyarmu ta shaida wa wakilinmu cewa, marigayiyar ta fara kwanciya ne a Federal Staff Hospital da ke Abuja, inda daga bisani a ka mayar da ita can Kano din.

Majiyar ta cigaba da cewa, gabanin kwanciyar Marigayiya Hauwa jinyar, ta yi fama da lalurar a tsai-tsaye ne, inda a ka lura da cewa, ta rame sosai.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 330

- Advertisement -

Daya daga cikin masu ruwa da tsaki na Kannywood da ke Kaduna kuma jarumi, sannan daraktan finafinai, Malam Al-Amin Ciroma, ya shaida wa wakilinmu cewa, marigayiyar ta rasu ne da misalin karfe tara na daren Larabar kuma za a yi jana’izarta da safiyar Alhamis din nan.

Tuni dai abokan sana’arta su ka shiga aika wa da sakonnin ta’aziyya ga juna a kafafen daban-daban, musamman ma zauren nan na masu ruwa da tsaki a masana’antar shirin fim din Hausa, wato Kanyywood Vanguard da kuma sauran kafafen sadarwa na zamani.

Hauwa Maina ta rasu ta bar ’ya’ya biyu, mace da namiji.

HausaLeadership

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.