Labarai

Yadda Fitaccen Ɗan Ƙwallo Ya Angwance Da Jarumar Fim

 A ranar Juma’a, 18 ga watan Yunin shekarar 2021 ne aka ɗaura auren fitaccen ɗan wasan Ƙwallon Ƙafar nan na yankin Arewacin Najeriya, wato Abdullahi Shehu da Amaryar sa, jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wato Naja’atu Muhammad Suleiman, wadda aka fi sani da ‘Murjanatu Ƴar Baba’.

An dai ɗaura Auren ne jim kaɗan bayan idar da Sallahr Juma’a a garin Kano.

Amarya Naja’atu Muhammad Sulaiman dai, wadda ake wa laƙabi da Murjanatu Ƴar Baba, ta fara fitowa a Fina-finan Hausa tun ba ta wuce shekaru 10 ba a duniya. Kuma ta samo sunan Murjanatu Ƴar Baba ne, a dalilin rawar da ta taka a cikin Fim ɗin Murnajatu Ƴar Baba tare da Amude Booth wanda Darakta Ashiru Nagoma ya bayar da Umarnin sa.

Kuma bayan Fim ɗin Murjanatu Ƴar Baba, ta fito a cikin wasu fina-finan da su ka haɗa da, AUREN GAJA, HAKKIN RAI, HARIRA da wasu da dama.

Kuma ga duk wanda ya san jarumar a baya-bayan, ya san ba ta da wata babbar ƙawar da ta wuce jaruma Maryam Yahaya.

 Daga
NAGUDU TV

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: