Kiwon lafiya

Yadda ciwon sikila ya hana ni cimma burina na aure’

Idan ka kalli Aisha, wata matashiya mai shekara 28 da haihuwa, ba ta da wani bambanci da sauran matasa mata da ke harkokinsu na yau da kullum.

Ma’aikaciyar gwamnati ce a daya daga cikin biranen arewacin Najeriya; ga ta son-kowa-kin-wanda-ya-rasa kuma kamar sauran mata da suka kai shekarunta, tana da burin yin aure ta hayayyafa.

Ma’ana, a wajenta—kamar yadda lamarin yake a wajen matasa maza da mata a tsakanin al’ummomi da dama a sassa daban-daban na nahiyar Afirka—aure muhimmin lamari ne.

Sai dai kuma har yanzu hakarta ba ta cimma ruwa ba, saboda samari bila adadin sun fito suna so su aure ta, amma da sun ji larurar da take fama da ita sai su cika rigarsu da iska. Tana fama ne da larurar amosanin jini, wato sikila.

“Na tsinci kaina a wani yanayi [da nake ji kamar] ba ni da wani amfani a duniya—idan har zan ci gaba da rayuwa ba tare da na samu [abokin zama] ba, rayuwata ba ta da amfani”, inji Aisha.

Aisha ce ta uku a jerin yara biyar da aka haifa a gidansu, kuma uku daga cikin ‘yan uwan nata ma na dauke da larurar ta amosanin jini. Sai dai daya daga cikinsu ya riga mu gidan gaskiya shekaru kadan da suka gabata.

Mahaifiyarsu ma, wacce yanzu shekarunta 60 da haihuwa, ta yi fama da cutar tana karama.

Aisha Bello Yusuf, mai fama da larurar amosanin jini

Kyama, kyara, tsangwama

Sau da dama dai lalurar kan yi dabaibayi ga rayuwar masu fama da ita ta fannoni da dama, har ma ta kan janyo masu kyama da tsangwama, ko tsana, hatta ma daga danginsu.

Mai yiwuwa wannan kyama ce ma ta hana Aisha cimma burinta na ganin wata rana tana rike da danta na cikinta.

“Wadanda na sa ran zan aura suna da dan yawa, amma abin bai yiwu ba.”

“Sau da dama idan manemana sun zo idan na fada masu gaskiya cewa ina dauke da ciwon sikila, su kan yi tunanin ba za su iya aure na ba”.

Yara 150,000 ake haifa da larurar

Ba Aisha da ‘yan uwanta ne kadai ke fama da wannan wahala ba: wata kididdiga da masu fafutukar wayar da kan al’umma game da ciwon sikila suka fitar ta nuna cewa a Najeriya, kimanin yara 150,000 ake haifa a kowace shekara da lalurar, wato kimanin rabin wadanda ake haifa da ita ke nan kowace shekara a fadin duniya.

Sai dai kuma cutar ta fi addabar al’umma a kasashen nahiyar Afirka, inda takan shafi kashi biyar cikin 100 na yaran da ake haifa.

‘Ana yanka katako’

Masu fama da ciwon kan koka da matsanancin radadi da ciwo a cikin kashi. A wasu lokutan takan shafi wasu gabobi ko magamar kasusuwan jikin dan’adam.

A’isha ta bayyana yadda take ji a duk lokacin da ciwon ya taso mata.

“Ciwo ne wanda [kan jefa mu cikin] matsanancin hali, za ka dinga jin kamar kafinta na yanka katako—za ka dinga jin kashin jikinka, ko ina yana maka ciwo.

“[Mahaifiyata] sikila ce; sau da dama na kan tambaye ta, na ce ‘Mama, ke kin san zafin haihuwa, don Allah da gaske ne cewa ciwonmu zafinshi ya fi na nakuda?’

“Amsar da ta ba ni [ita ce], gara ta haihu sau 12 da ta yi ciwo sau daya”.

Wasu daga cikin mutane a kasashen da aka fi fama da larurar kan yi camfe-camfe game da yaran da ke dauke da ita, abin da kan sa a rika kyarar su.

A’isha ta ce domin samun saukin tashin hankalin da takan fada sakamakon kyama ko kyara, takan halarci wani taron masu larura irin tata, inda ake ba su shawarwari.

Shawarwari

Halima Usman Nagado, wadda ita ma danta na farko ya rasu yana da shekara 11 sakamakon larurar, na cikin wadanda kan taimakawa masu fama da ita da shawarwari.

Don haka ne ma ta kafa wata gidauniya, inda takan kuma taimaka masu magunguna; takan shiga kauyuka domin wayar da kan al’umma game da cutar ta sikila, da kuma kai masu tallafi.

“Na ga cewa ya dace mu da muka san yadda abin yake mu fito mu yi fadakarwa mu ja kunnen mutane mu kuma yi masu gargadi, cewa a san yadda za a yi a daina yada wannan ciwo”, inji Hajiya Halima, wadda ta kara da cewa, “yadda za a daina yada wannan ciwo shi ne mutum ya je ya duba jinsin jininsa sau daya, sau biyu, sau uku kafin ya yi aure.

“Su kuma wadanda suke da shi mu ga yadda za mu yi mu taimaka wa rayuwarsu.”

Saboda ta gaza cimma burinta, Aisha kan rasa abin da ke mata dadi a duniya.

“Na kan zauna na yi kuka, na yi kuka, domin ni ma haka na tsinci kaina”.

Aisha Bello Yusuf
Na kan zauna na yi ta kuka…

A cewar Halima Usman, aure babban yaki ne ga matasa masu fama da cutar sikila.

“Idan an zo neman su sai a rinka ganin kamar kawai wahala za a yi, ko kuma jinya za a yi ta yi har abada.”

Sai dai ta kara da cewa babu abin da mai fama da cutar sikila ba zai iya cimmawa ba a rayuwa, sannan ta ce akwai dubarun da masu cutar za su iya amfani da su su samu saukin rayuwa (duba jerin da ke kasa).

About the author

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement