Yadda Buhari Yake Lashe Zabe A Yanar Gizo Haka Zai Lallasa Atiku A Zaben Zahiri -PMBCN

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yadda Buhari yake lashe zabe a yanar gizo haka zai lallasa Atiku a zaben zahiri -PMBCN

Wata kungiya mai fafutukar wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari damar sake mulkar kasar a zaben 2019, mai suna President Muhammadu Buhari Continuity Network (PMBCN) ta ce yadda shugaban kasa Buhari ya lashe zaukan yanar gizo, haka zai lallasa Atiku Abubakar a zaben zahiri da za a gudanar a shekarar 2019.

Talla

Daraktar kafofin sada zumunta da watsa labarai ta kungiyar, Miss. Elsie Ijorogu Reed,ce ta bayyana hakan,a zantawarta ta wayar tarho da manema labarai, a yayin da ake kaddamar da kungiyoyi 50 da zasu taimaka wajen yakin zaben Buhari a 2019, wanda ya gudana a otel din Nicon Luxury da ke Area II, Abuja.

Miss. Elsie Ijorugu Reed, ta ce:”Zaka yi mamaki yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke lashe kusan dukkanin wasu zabukan yanar gizo da aka shirya a shafuka daban daban, ciki kuwa har da shafin wata kungiya da ke yakin zaben Atiku Abubakar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

“Idan kuwa har Buhari zai samu nasarar lashe zabe a shafin yakin zabe dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, ke nan, ko a zaben zahiri da za a gudanar a 2019, Buhari zai lallasa Atiku da tazarar kuri’u mai yawa.” inji ta.

Kungiyar ta PMBCN ta bayyana cewa, babu ta yadda za’ayi al’ummar shiyyar Kudancin kasar nan su zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar, duba da irin manyan ayyukan raya kasa da shugaban kasa Buhari ya kaddamar a shiyyar, kama daga hanyoyi, gadoji da dai sauran fannonin more rayuwa.

Miss. Elsie Reed ta kuma yi kira ga daukacin magoya bayan shugaban kasa Buhari da jam’iyyar APC,da su kauracewa amfani da kalaman batanci da cin zarafin abokan hamayya da sunan adawa, tana mai cewa,”idan kana son jawo mutane a jikinka, hantararsu ba shine hanya mafita ba. Zaka yi masu kyawawan kalamai da kuma warware masu kullin da suka kasa kwancewa, da hakane zaka samu damar karkato da tunaninsu amma ba da kalaman batanci ba.”

Dangane da ayyukan kungiyarsu ta President Muhammadu Buh

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: