Yadda Ake Kunun Shinkafa Da Madara

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Assalamu alaikum Uwargida. Yaya sanyi? Tare da fatar ana girka wa manyan gobe girkin da zai kara musu lafiya da kuzari. A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa mai madara. Kasancewar ana yawan rage abinci musamman ma idan farar shinkafa ce, wani lokaci ana rasa yadda za a yi da ita. Hakan ya sanya a yau na kawo muku wani salon sarrafa wannan ragowar shinkafar. A sha karatu lafiya. Shan wannan kunun na rage wa manyan gobe yin mura a wannan yanayin sanyi.

Abubuwan da za a bukata

• Dafaffiyar shinkafa fara

• Madara

• Citta karama kwaya daya

• Sukari

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 2

• Kwayar tafarnuwa daya

• Ruwa

Hadi

A kankare danyar citta sannan a jajjaga ta a zuba ruwa a tace a ajiye a gefe. Sannan a bare tafarnuwa kwaya daya a jajjaga a zuba ruwa a tace. Sannan a hada ruwan tafarnuwar da na cittar a waje daya.

A tafasa shinkafa har sai ta yi laushi, sannan a debo garin madara daidai wadata a zuba a cikin ruwan cittar da tafarnuwar sannan a gauraya.

A zuba ruwan madarar a cikin shinkafar sannan  a dora a kan wuta.  Idan kunun ya fara kauri sannan a zuba sukari yadda ake bukata sai a sauke.

Za a iya shan wannan hadin da soyayyiyar ayaba ko zuma da kosai ko ’ya’yan itatuwa. A sha dadi lafiya!

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.