Cin Hanci da Rashawa

Yadda Aka Kama Wasu mutane Biyu Barayi Da Suka Saci Awaki 15 a Osun 

Yadda Aka Kama Wasu mutane Biyu Barayi Da Suka Saci Awaki 15 a Osun

 

Rundunar ‘yan sanda ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin barayin dabbobi ne da ake zargin sun kware wajen satar awaki daga garuruwan Osogbo, Ikirun, Obagun, Iree, Eripa, Otan-Ayegbaju da Ila a jihar Osun.

 

Jami’an ‘yan sandan da ke sintiri a babbar titin Safer a lokacin da suke tsayawa suna binciken ababan hawa a yankin Odeomu-Sekona, sun cafke mutanen biyu; Naheem Ibrahim mai shekaru 46; da Suraju Isiaka, mai shekaru 33, a lokacin da suke kokarin kwashe dabbobin zuwa Legas a cikin wata mota kirar Lexus SUV.

 

A binciken da ‘yan sanda suka yi, an gano cewa wadanda ake zargin sun mallaki awaki guda 14 da matacciyar akuya daya, domin sayar wa abokan cinikinsu a jihar Legas.

 

Bayan gano dabbobin da aka sace, ‘yan sanda suka kama wadanda ake zargin nan take zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Osogbo domin yi musu tambayoyi da kuma bincike.

 

Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin suna kai hari ne a daidai lokacin da masu awakin suka kwanta barci da kuma masu gadin dare da ke aikin sa ido kan al’ummomin ba su fara aiki ba.

 

Bincike ya nuna cewa mazauna wadannan al’ummomi sun yi ta mamakin yadda awakinsu ke bacewa ba tare da an gano inda suka shigo ba, wani lokaci kuma suna zargin juna da yin satar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola, wanda ya tabbatar da kamen, ya ce wadanda ake zargin sun nufi Legas ne a cikin wata mota kirar Lexus SUV tare da dabbobin da suka sace daga al’ummomi daban-daban a lokacin da ‘yan sanda suka kama su.

“Da aka yi musu tambayoyi, sun amsa cewa sun sace awakin daga wurare daban-daban a Osogbo, Ikirun da lla-Orangun domin a sayar da su ga wata lya Bisola a Mile-12, jihar Legas. Bugu da kari, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun yi aiki a jihar Osun tun a shekarar 2019.”

 

Ta ce wadanda ake zargin sun amsa cewa lokacin aikin su ya kasance tsakanin karfe 8 na dare zuwa karfe 10 na dare kafin masu gadin dare a wurare daban-daban su zo bakin aikinsu, inda ta ce ana sayar da awakin ne tsakanin Naira 5,000 zuwa Naira 10,000.

 

Daga Baba Waziri Net ✍️

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.