Labarai

Yadda aka bindige mutum 48 a yankin Maradun, mahaifar gwamna Matawalle

Da yammacin nan ne aka yi jana’izar mutum 48 waɗanda ‘yan bindiga su ka bindige cikin yankin Faru da ke Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Yayin da jaridar Daily Post ta wallafa cewa mutum 42 aka kashe, PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa mutum 48 ne aka kashe.

Maharan sun kai harin ne a garuruwan Tsauni, Gidan Gaishe, Gidan Adamu, Gidan Maidawa da kuma Ƙyara. Sun kai harin ranar Alhamis cikin daren wayewar Juma’a.

PREMIUM TIMES Hausa ta ji daga wani wanda ya halarci jana’izar, a garin Faru da ke karkashin Sarkin Yamman Faru cewa, “Mutum 48 mu ka yi wa Sallar Jana’iza kafin La’asar ɗin nan.”

Maharan sun kuma ƙona gidaje saman sun saci kayan abinci.

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu, ya shaida wa Katsina Daily Post cewa “mutum 35 ne aka kashe.”

Karamar Hukumar Maradun dai can ne mahaifar Gwamna Bello Matawalle, wanda makonni biyu da su ka gabata ya ce ya koma APC ne don a daina kashe mutane a Jihar Zamfara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: