Kannywood

Yadda Adam Zango ya so ya auri Ummi Rahab – Yasir Ahmad

MATASHIN nan da ake cewa shi ne ya ɗaure wa Ummi Rahab gindi har ta yi wa Adam A. Zango barazanar za ta tona masa asiri ya maida kakkausan martani kan maganganun da ake yaɗawa. A ciki, ya ƙaryata Zango a kan iƙirarin wai bai taɓa yin soyayya da jarumar ba, da kuma batun wai ya rabu da ita ne saboda ba ta yi masa biyayya.

Matashin, mai suna wato Yasir M. Ahmad, wanda ya ce shi ɗan’uwa ne ga jarumar, ya yi magana kan batun cewa Rahab ta butulce wa Zango bayan ya ɗaga tauraruwar ta a Kannywood, da kuma batun wai ba ta da iyaye.

Ta cikin wani saƙon bidiyo da ya fitar a yau a Instagram mai tsawon minti 20, Yasir ya bayyana cewa faro labarin sa da cewa shi ne silar shigar Rahab harkar fim, ba Zango ba.

A bidiyon, wanda wakilin mujallar Fim ya kalla a tsanake Yasir ya ce, “Na farko dai, Adamu ba shi ya kawo Ummi industiri ba, kuma Adamu ba shi da alaƙa ta ‘family’ ko wani dangi ko na nesa ko na kusa. Hasali ma sun haɗu a fim ɗin ‘Ummi’ ne; ta zo ne, shi ma ya zo, don a lokacin ba zan taɓa mantawa ba fim ɗin ‘Ummi’ ma kamar lokacin za mu yi tafiya ne sai Mu’azzamu Idi Yari, a lokacin ya zo gurin mu ni da yarinyar nan, ya ce don Allah ya na so ta yi masa aikin nan, don a lokacin tafiya za mu yi, za mu je biki ne.

“To, sai Umar Kanu, mijin Fati Muhammad, shi ne ya ba shi lambar mu ya zo ya same mu har tasha, ya nemi wannan alfarmar, aka zo aka yi wannan fim ɗin, ‘Ummi’.

“A nan mu ka fara ganin Adamu, ita ma a nan ta fara ganin shi, don a lokacin ya yi aiki da yarinyar a fim ɗin ‘Ummi’, ya ga masha Allah ta yi aiki mai kyau, wanda a lokacin wannan fim ɗin ta fara yi.

“To, bayan an gama aikin ne kuma mu ka yi musayar lambobin waya. To wannan dai shi ne haɗuwar mu ta farko da Adamu.”

Ya ƙara da cewa fim ɗin ma da jarumar ta fito ba na Zango ɗin ba ne, na Mu’azzamu idi Yari ne, shi ne darakta da kuma furodusa Abdul Amart.

Yasir M. Ahmad ya na bayani a cikin bidiyon da ya fitar

Yasir ya ci gaba da faɗin, “Bayan sati biyu, a lokacin sai na ga wayar Adamu ya kirawo ni. Ya na ce min yarinyar nan sun saba da ɗan sa Haidar, ya ce don Allah ya na neman alfarma idan dai ta samu hutu ya na so ta zo gidan sa ta yi hutu, don a lokacin ma ta na zuwa makaranta. To bayan sun yi hutu, kamar yadda aka yi alƙawari, ni da kai na na je har Kaduna na kai masa yarinyar nan. A can na bar ta. Bayan sati biyu har wa yau sai ya dawo da ita gida.”

Yasir ya kuma ƙaryata raɗe-raɗin da ake yi na cewar Rahab ba ta da iyaye, ya ce ba haka ba ne.

“Maganar da ake yi na cewar Ummi ba ta da mahaifiya ko mahaifi, maganar ba haka ta ke ba. Hasali ma akwai lokacin da Adamu ya shirya za shi Saudiyya, ya zo ya karɓi lambar mahaifiyar yarinyar nan a lokacin, ya ce mani idan sun je Saudiyya za su gaisa. Na ɗauka na ba shi, su ka je Saudiyya da shi da Afakallahu da Rarara, su ka je.

“Bayan sun yi aikin su na Umara su ka kirawo ta a waya, don a lokacin ma ita ta zo ta same su a masaukin su, su ka yi magana. A lokacin ma har ya nuna sha’awar ya na so ya aure ta. Kuma babar ta a lokacin ma ta kira ni ta yi mani bayanin abin da ya faru.”

Ya ce lallai a lokacin akwai soyayya tsakanin jarumin da jarumar, don Zango ya nuna ya na ƙaunar ta.

Ya ce, “Don ni ma wannan abin na kula da shi, shi ya sa a lokacin ba na iya yin wani abu, don na san a lokacin akwai ƙauna.

“Akwai lokacin da Ali Nuhu ya kira ni a lokacin ina tare da ita, ya ce min, ‘Yasir ne?’ Na ce, ‘E.’ Sai ya ce don Allah ya na so za su yi aiki da wannan yarinyar Ummi, wani aiki ‘Labiba’; zai tura min sikirif a Kaduna. Na ce masa ba matsala.

“A lokacin kuma ta yi finafinai dai kamar guda biyar ne ko shida ne, irin ta yi ‘Labiba’, ta yi ‘Sadakar Yalla’, ta yi ‘Watan Wata Rana’, irin su ‘Gudan Jini’. To a lokacin wannan finafinan su ne wanda ta yi kuma a lokacin duk waɗannan finafinan ba su fito ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: