Get New DJ Mixes
Labarai

Yace A Kai Kasuwa Baya Neman Tikitin Takara A jamiyyar PDP – Dangote

Martanin da Aliko Dangote ya mayar wa da PDP dai bazai yi musu dadi ba, saboda a cewarsa, sun zaqe kafin ma su tuntube shi.

Wannan na zuwa ne a bayan kokarinsu na kakaba wa shi dan kasuwar tikitin jam’iyyarsu da a yanzu ta rage tagomashi, saboda munanan badakalolida ake ta tono wa.

A makon nan ne dai aka jiyo kishin-kishin wai jam’iyyar PDP ta sami matsaya kan ko wa zaiyi mata takara a zaben 2019.

 

Dangote dai hamshakin mai kudi ne da ya dade yana taimakawa masu takara da biliyoyin nairori, musamman a PDP.

Sai dai a gabanin zaben 2015, an gano dan kasuwar ya bar Najeriya a ranar bikin tara kudin kamffe na zaben, bai kuwa baiwa Goodluck Jonathan din ko sisi ba, sai cewa yayi zaiyo waya.

Bayanai daga baya sun tabbatar dai Aliko Gote ya baiwa APC da su Tinubu makudan Daloli ne domin gudummawarsa ga takarar shugaba Buhari.

Kin taimakawa PDP da yayi, baya rasa nasaba da koken arewa kan Boko Haram, wariya da Goodluck ne nuna wa karara a wancan lokacin, da ma takura wa abokan Dangoten musamman Sunusi Lamido Sanusi da su Nasir El-Rufai.

Da kuma zanyar cin hanci da ya mamaye mulkin na PDP, dadi da yaga katin da Obasanjo yayi a bainat jama’a, don kuntata wa PDP.

Kwatsam sai wai gashi saboda PDPn taga babu mulki a hannu, babu kuma kudin kamfe, ta dauko shi wai ya kashe kudinsa yayi takara da hamayya ma da watakil Janar Buhari, wanda ka iya jefa kadarorinsa cikin fushin gwamnati, ko ma fushin talakawa.

 

Souce In Mikiya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.