Shugabannin kasashen Najeriya da Angola da Zimbabwe da Benin, da Algeria na da abubuwan da suke kamanceceniya, wato rashin yarda da tsarin kiwon lafiyar kasashensu.
Ta fuskar lokutan da suka shafe suna jinya a kasar waje, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari mai shekara 74, shi ne na farko a cikinsu, amma a shekarun da suka gabata dukkan wadannan shugabannin sun ketara wasu kasashen don duba lafiyarsu.
A lokuta da dama suna tafiya su bar asibitoci ba isasshen kudin da za a samar da magunguna, wanda akasarin ‘yan kasar suka dogara da shi.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, a shekarar 2010, matsakaicin kudin da ake kashe wa lafiyar dan Afirka daya shi ne dala 135, idan aka kwatanta da dala 3,150 na kasashen da suka fi samun kudin shiga.
A cewar wata kungiya mai sa ido a harkar lafiya, misali a kasar Zimbabwe, an sha samun yankewar magungunan da ake tsananin bukatarsu irinsu na kashe radadin ciwo da kuma masu yaki da kwayoyin cuta a asibitocin gwamnati .

Kamar Najeriya, tsarin kula da asibitocin gwamnati ya yi muni,” saboda rashin wadataccen kudi, in ji editan BBC na Abuja.
Tsarin inshorar lafiya na ma’aikatan gwamnti da kuma sauran ma’aikata masu zaman kansu, ya bai wa wasu mutane samun damar magani na asibitoci masu zaman kansu, amma mutane da yawa sun dogara ne da wanda gwamnati take samarwa.
A dukkan wadancan kasashen, wadanda suke da kudi ne suke samun cikakkkiyar kulawa a asibitoci masu zaman kansu, amma a wasu lokutan ana ganin cewa an fi samun hakan a kasashen ketare.
Shugaban Najeriya ya shafe sama da uku hudu a Londan yana jinyar cutar da ba a bayyanata ba, wacce ta haddasa ce-ce ku-ce a kasar.
Ba kamar irin ta takwaransa Umaru Musa Yar’Adua ba, wanda ya tafi kasar Saudiyya don ganawa da likita, shugaba Buhari ya bar wa mataimakinsa ragamar mulkin kasar, amma hakan bai hana mutane yin suka ba.
19 ga watan Janairu – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”
5 ga watan Fabrairu – ya nemi Majalisar Dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya
6 ga watan Yuli- Aisha Buhari ta ce, “yana samun sauki sosai”
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, wanda yake mulki tun shekarar 1980, shi ma ya sha suka daga abokan hamayyar siyasa, na jan ragamar kasar “daga gadon asibiti”, bayan tafiyar da ya yi Singapore domin duba lafiyarsa karo na uku a wannan shekarar.
A watan Mayu ne gwamnatin Angola ta bayyana cewa, Jose Eduardo dos Santos, wanda yake shi ne shugaban kasar na tsawon shekara 38 da ta gabata, ya je Spaniya don duba lafiyarsa.
Amma a bangaren Najeriya, gwamnati ba ta bayyana wani abu game da halin lafiyar shugaban ba.
Batun rashin lafiyar shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika, mai shekara 80, sanannen al’amari ne tun tsawon lokaci.

Kamfanin dillanci labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, a shekarar 2013 ne ya sha fama da ciwon zuciya, inda ya yi amfani da keken guragu wajen zuwa kada kuri’a, daga baya kuma ya tafi jinya a sibitin Faransa.
A watan Nuwambar da ya gabata ne ya koma gida, a matsayin daya daga cikin abin da gwamnati ta kira “Takaitaccen duba lafiya”
Amma abin tambaya a nan shi ne, me yake jan hankalinsu zuwa wata kasar jinya?
Ba mu yi mamaki ba, babu wani kakakin shugaban kasa da ya fito ya ce suna hakan ne saboda an fi samun cikakkkiyar kulawa a kasashen ketare.
Ko da yake, mai magana da yawun Mista Mugabe, ya yi martani game da tafiyar da shugaban ya sha yi zuwa Singapore, inda a watan Mayu ya tsaya kai da fata cewa, hakan ba ya nufin ya juya wa tsarin lafiya na Zimbabwe baya ne.
Jaridar kasar ta rawaito inda George Charamba yake cewa, “Ba likitocin Zimbabwe ba ne kawai suke duba shugaban, a zahiri baki ne, baki sosai.”

Batun dai kawai shi ne, a wata kasar ne kawai za a iya duba matsalar idon da Mista Mugabe ke fama da ita, “wacce take bukatar wadanda suke da kwarewa a fannin lafiya”.
Mai magana da yawunsa ya ce, saboda wannan matsalar ce tasa, wani lokaci Mista Mugabe yake lumshe idonsa a lokacin da ke gabatar da taro, sai a ga kamar yana bacci.
Wani babban likita a Najeriya Osahon Enabulele, ya ce, batun wadannan tafiye-tafiye ba kawai suna nuna gazawar likitoci na gida ba ne, suna ma yin zagon kasa ga bangaren lafiya na kasar.
Ya kira wannan halayya da ‘yin tafiye-tafiye don neman lafiya, ya kuma ce hakan da shugabanni ke yi yana jawowa kasar asarar miliyoyin daloli.
A shekarar 2013, ya kiyasta cewa ‘yan Najeriya suna kashe dala biliyan daya a kasashen waje don neman lafiya, inda ya ce a yanzu kam wannan adadi zai iya nunka haka.
Idan aka kwatanta, kasafin kudin da gwamnatin tarayya ta yi na shekarar 2016 an ware wa bangaren lafiya dala miliyan 800.
Dr Enabulele, wanda mataimakin shugaban kungiyar likitocin kasashe rainon Ingila ne, ya ce kudin da ‘yan Najeriya ke fitarwa zuwa wasu kasashe don neman lafiya zai isa a bunkasa tsarin lafiya a kasar.
Ya ce a game da hakan, manyan likitocin Najeriya na ketarawa kasashe don samun cikakkkiyar kulawa, abun kuma na kara tabarbarewa.

Dokta Enabulele ya kara da cewa, yana fata shugaban Najeriyar ya samu lafiya, yana ganin zai iya samun dukkan kulawar da yake bukata a kasar.
Babban abin da ya kamata a lura shi ne, rashin wadataccen kudi a bangaren lafiya shi ne matsalar.
Har wa yau, shugabanni ba lallai ne su mayar da hankali wajen bunkasa asibibitoci ba, idan dai har za su rinka tafiya wasu kasashe jinya.
Wata kila za su iya daukar darasi daga wurin shugaban Sudan Omar al-Bashir.
A watan Janairu ne, ya yi wani abu da kamfanin dillanci labarai ya bayyana a matsayin “Ciwon zuciya,” a wani asibitin da ke babban birnin kasar, Khartoum.
Duk da cewa asibitin na kudi ne ba na gwamnati ba.
Source BBCHausa
Add Comment