Labarai

Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Ba a taba jin Shugaba Buhari da Osinbajo ba, tun bayan da suka lashe zabe a shekarar 2015

Rawar da Fiye da Farfesa Yemi Osinbajo yake takawa a matsayin mukaddashin shugaban kasa sakamakon rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya shafe watanni a wajen kasar na ci gaba da jan hankalin jama’a. Yayin da wasu ke cewa yana taka rawar gani, wasu kuwa cewa suke yi yana dari-dari.

Rashin lafiyar shugaban, wanda ba a bayyana takamaiman abin da ke damunsa ba, da kuma halin da kasar ke ciki ya sa fagen siyasar kasar daukar dumi a wasu lokuta.

 

Akwai wadanda suke ganin babu abin da ya sauya bayan da Mista Osinbajo ya fara tafiyar da kasar a watan Janairun da ya gabata.

Masu irin wannan tunanin su kan kafa hujja da yadda Farfesan ya jira sai da ya samu umarni daga Shugaba Buhari gabannin ya sanya a kasafin kudin kasar a watan Yuni.

“Akwai wasu abubuwa da za mu ce shi ne ya kirkiro su, misali akwai abubuwa da ya yi musamman ta fuskar tattalin arziki wato yadda ya yi hobbasa wajen farfado da darajar naira,” in ji Malam Kabiru Danladi Lawanti na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Ya ci gaba da cewa, “Mutum ba zai yanke hukunci gaba daya ba, tun da an ce duk wani muhimmin mataki da zai dauka sai ya tuntubi Shugaba Buhari.”

“Idan ban da tsare-tsare ta fuskar tattalin arziki, to babbu wani abu da za a ce Mista Osinbajo ya yi daban daga Buhari,” in ji Malam Kabiru.

Sai dai ana sa bangaren, Malam Mahmud Jega, mataimakin babban editan jaridar Daily Trust, ya ce mukaddashin shugaban “yana taka tsan-tsan.”

Ya ce ba ya tsammanin akwai wani mataki da ya dauka nasa na kashin kansa ba wanda Shugaba Buhari ya tsara ba.

“A duk tsawon makonnin nan da Osinbajo yake rikon-kwarya, gaskiya yana sassarawa ne ta gefe, ba ya taba manyan abubuwa na babban aikin gwamnati ko na siyasa, ko kananan abubuwa ma ba duka yake taba wa ba,” in ji Jega.

Daga nan ya ba da misalin yadda mukaddashin shugaban ya kasa nada ministoci duk da cewa Shugaba Buhari ya aike da sunayensu wadanda majalisar dattawan kasar ta amince da su, “amma a rantsar da su, a ba su mukami ya gagara”.

Yemi Osinbajo ne ke tafiyar da al’amura tun bayan tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari

Game da batun tattalin arziki da ake cewa Mista Osinbajo ya tabuka wani abu yayin da Buhari yake jinya, Mahmud Jega ya ce aikinsa ne a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa.

“Mataimakin shugaban kasa shi ne shugaban da ke kula da majalisar tattalin arzikin kasa wadda ta kunshi gwamnoni da wasu manyan ministoci da kuma gwamnan babban bankin Najeriya,” in ji shi.

‘Dole ne Osinbajo ya yi taka tsantsan’

Malam Kabiru Lawanti ya ce yana ganin mukaddashin shugaban yana tsoron zakewa ne saboda iya siyasa da kuma neman karbuwa ga kowanne bangare na kasar.

“A takaice Osinbajo ya zama cikakken dan siyasar Najeriya, wanda yake taka tsan-tsan da yadda siyasar bangaranci da addini ta ke tafiya a Najeriya.”

“Yana jin tsoro ne saboda kada ya zake da yawa a ce yana so ya gaje kujerar Shugaba Buhari. Idan ka duba abin da ya faru da Jonathan lokacin jinyar ‘Yar Adua, to dole Osinbajo ya yi taka tsantsan.

Ya raba kafa ne idan Buhari ya dawo su ci gaba da tafiya tare idan ma Buhari bai dawo ba to akwai mutanen da bai ba ta da su ba,” in ji shi.

Farfesa Osinbajo ne mutum na biyu da ya taba rike mukamin mukaddashin shugaban kasa a siyasar Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ne ya fara rike mukamin yayin da marigayi Shugaba Umaru ‘Yar Adua yake jinya.

Ba a taba jin Shugaba Buhari da Osinbajo ba, tun bayan da suka lashe zabe a shekarar 2015, ko da yake, akwai wasu masu sharhi da suke ganin a kwana a tashi, wata ran za a iya jin kansu.

Yayin da Osinbajo ya kai wa Shugaba Buhari ziyara domin duba shi a Landan, shugabannin biyu sun shafe fiye da sa’a guda suna tattaunawa, wacce ita ce ganawar su ta farko tun bayan tafiyar shugaban jinya sama da wata biyu da ya gabata.

Har yanzu ba a bayyana cutar da shugaban ke fama da ita ba, ballantana lokacin da zai dawo don ci gaba da tafiyar da al’amuran kasar.

Sai dai na kusa da shi na cewa nan ba da jimawa zai koma gida.

 

Bbchausa Abuja

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement