Labarai

Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Masu zanga-zangar ba su samu damar ganawa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba, saboda gwamnatinsa ta hana gudanar da macin

Wasu mata sun gudanar da zanga-zanga kan yadda al’umma a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ke yin wasarairai da matsalar karuwar fyade.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Hajiya Aisha Dan kani ta ce sun gudanar da zanga-zangar ce don zaburas da jama’a kan alhakin da ya rataya a wuyansu na shawo kan karuwar fyade.

 

Zanga-zangar wadda tsoffin daliban makarantar St. Louis suka shirya amma gwamnatin jihar Kano ta ce kada a yi, ta ci gaba da gudana duk da rashin samun damar ganawa da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje kamar yadda aka tsara.

Likitoci dai sun ce fyade na karuwa maimakon raguwa a Kano, inda wata kididdiga ke nuna cewa tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2017, an samu rahotannin aikata fyade fiye da 700 a jihar, kuma kashi 45 cikin 100 na wadanda aka yi wa fyaden yara ne ‘yan kasa da shekara 10.

Matan wadanda suka jure wa ruwan saman da ake yi yayin zanga-zangar da safiyar ranar Talata na dauke da rubuce-rubucen da suka hadar da “kada a yi fyade” da kuma “a rika hukunta masu fyade”.

Aisha Dan kani ta ce al’amarin yana ba ta kunya…kuma dole ne wasu daga cikin al’umma su tashi tsaye don magance karuwar fyade.

A cewarta, kamata ya yi a ga jama’a sun kai ruwa-rana a kan wannan laifi don kawo sauyi amma sai ga shi hakan ba ta samu ba.

Ta ce “So muke a sanya batun magance fyade a gaba. Kamar batun shigar da kara kan zargin fyade, ba zai yiwu mutumin da yake kokawa wajen samun abin da zai ci ka ce ya zo kotu ko caji ofis sau talatin ko hamsin ba.”

“Kamata ya yi gwamnati ta samar da wata manufa ta yadda za a hana mutane barin kango a tsakanin gidaje tsawon shekara goma ba tare da ana sa ido a kai ba, kuma babu wanda zai yi magana.”

Haka ita ma wata likita, Dr. Safiya Al-hakim Dutse wadda tana cikin masu gudanar da zanga-zangar ta ce alhaki ne na iyaye da al’umma kuma dole ne su tsaya su kula da ‘ya’yansu.

“Kada a rika barin matasa a baya, al’umma su kafa kwamitoci tare da limamai da masu unguwanni da sauran masu fada-a-ji don a rika fadakar da su, don sa ido kan abubuwan da ke faruwa a unguwanninsu,” in ji ta.

 

Souce In Bbchausa

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.