‘Yan sanda a kasar India sun ce sun cafke wani dattijo mai shekara 60 da ya hallaka matarsa ta hanyar bindigewa saboda bata gama abincin dare da wuri ba.
A daren Asabar ne Ashok Kumar ya dawo gida cikin maye, inda gardama ta kaure tsakaninsa da matarsa , kamar yadda wani babban jami’in ‘yan sanda Rupesh Singh ya shaida wa BBC a birnin Ghaziabad da ke kusa da Delhi babban birnin kasar.
An garzaya da Sunaina, mai shekara 55 zuwa asibiti bayan da ta samu rauni daga harbin bindigar da ta samu a ka, amma kafin a isa asibiti rai ya yi halinsa.
Mr Kumar ya amsa laifin da ya aikata, kuma yanzu haka yana cikin nadama, in ji Mr Singh.
” Mutumin ( Mr Kumar) ya saba shaye-shaye a kullum. A ranar Asabar ya dawo gida a buge, inda ya fara sa-in-sa da matarsa. Ta cika da bacin rai game da dabi’arsa, tana so ta yi masa magana a kai, amma ya bukaci ta kawo masa abinci da wurwuri,” in ji Mr Singh.
Ya kara da cewa ” Ya fusata da bata lokacin da ta yi kawai sai ya harbe ta”.
Wakiliyar BBC a birnin Delhi ta ce irin wannan cin zarafi da mata ke fuskanta a gidajen aurensu ba sabon abu bane a kasar ta India- yana faruwa a ko ina a fadin duniya- amma abinda ya banbanta India da sauran kasashe shine dabi’ar rashin fitowa fili a bayyana.
Add Comment