Kannywood

Ya Karyata Masu Cewa An Doke Shi A Ido – Ado Gwanja

Kamar yanda muka gani a wani dandalin sada zuminchi na facebook maisuna kannywood exclusive, sun post akan wasu mutane sun yiwa mawaki kuma jarumi Ado Gwanja dukan tsiya har sai da suka kumbura ma shi ido.

To mun kira Ado Gwanja dan jin gaskiyar lamari, amma sai yaba wakilinmu amsa da cewa: babu wasu mutane da suka zage ni agabana bare kuma su doke ni harda yi min rauni.

Duk wanda yace wani mugun abu yasame ni, to tabbas, hassadace wanda hausawa sukance ga mai rabo takice.

Ni da mutane mata da maza suke son ganina dan soyayya, tayaya za’ace sunyi min dukan tsiya? wannan hankali ba zai gamsu da haka ba. zanyi amfani da wannan damar naba al’umma shawara akan dan Allah su daina yada jita_jita.

Domin maganganun mu ababan a tambaye mune aranar gobe kiyama.

Kuma ina yiwa masoya albishir cewa ina nan lafiya, kuma inayi masu fatan alkairi a duk inda suke.

Inji Ado Gwanja.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.