Ya Kamata Mata Su Dogara Da Kansu, Kada Su Dogara Da Mazajensu Dari Bisa Dari, Cewar Jaruma Fati Bararoji
Fati Baffa Baroroji tsohowar jarumar finafinan Hausa ta shawarci mata ‘yan uwanta da su zama suna da hanyan dogaro da kai, kada su dogara dari bisa dari akan mazajensu.
Bararoji ta kuma kara da cewa yanzu zamani ya canja, domin ita yanzu tana tsaye ne da kafafuwanta domin tana da sana’oi masu yawa.
A cewar ta ya kamata mata su daina dogaro dari bisa dari akan mazaje domin rayuwa ta yi tsada kuma mazan ma yawancin su walakanci ne da su.
Daga Sani Twoeffect Yawuri
Add Comment