Labarai

Ya Kamata Ku Rage Son kuɗi, Gargaɗin Gwamnatin Tarayya Ga Matasan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta gargaɗi matasan da ke neman guraben aikin yi a ƙasashen waje da su yi taka-tsantsan, don kada su faɗa hannun masu fataucin mutane, The Cable ta ruwaito.

Memunat Idu-Lah, daraktar hulda da al’adu na kasa da kasa a ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu, ta bayyana haka ne a wata hira da NAN a ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta.

Idu-Lah, wacce ta shawarci matasa da su nemi aiki a cikin ƙasar nan, ta ce akwai shirye-shiryen ƙarfafawa daban-daban na gwamnatin tarayya wadanda za su iya ba matasa damar samun fa’ida.

“Ina ganin ya kamata mu hana matasa fita. Idan suna buƙatar tallafi, akwai wasu hukumomin gwamnati waɗanda aka ɗora wa alhakin samar da shirye-shiryen ƙarfafawa da yawa.”

“Hukumar kananan sana’o’i (SMEDAN) tana nan, da kuma shirye-shirye da yawa da gwamnati ta yi don taimakawa matasa don karfafa su.” In ji Idu-Lah

Ta kuma jawo hankulan matasa ƴan Najeriya cewa, ba komai ne dole sai da kuɗi ba, tana mai shawartar cewa, ya kamata ƴan Najeriya su zauna a gida domin haɓaka samar da kayayyakin gida da ya kamata ƴan ƙasa su sarrafa.

Ta kuma ƙara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari na iya kokarinta don ganin an farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da kuma tallafawa matasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: