Argentina ta ci gaba da fafutikar ganin ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018 inda ta sha da kyar a hannun Venezuela, wacce ke mataki na karshe, da ci 1-1 a wasan da suka yi a gidan Argentinar.
Dan wasan Venezuela Jhon Murillo ya soma jefa kwallo a ragar Argentina ko da yake kwallon da suka ci kansu bayan komawa daga hutun rabin lokaci ta sa Argentina ta samu maki daya.
Yanzu dai Argentina na matsayi na biyar a cikin kasashen da ke Kudancin Amurka kuma suna da sauran wasa biyu yayin da kasashe hudu da ke suka fi yawan maki suka cancanci zuwa gasar cin kofin duniyar – Argentina za ta fuskanci New Zealand.
Brazil, wacce tuni ta samu gurbin zuwa gasar, ta yi kunnen-doki 1-1 da Colombia.
Dan wasan gaba na Chelsea Willian ne ya ci wa Brazil kwallo ko da yake daga bisani dan wasan Monaco Radamel Falcao ya fanshe. Dan wasan tsakiya na Liverpool Philippe Coutinho ya shigarwa Brazil wasa bayan an yi nisa da wasan.
Uruguay tazakuda zuwa matsayi na biyu bayan ta doke Paraguay da 2-1 yayin da Peru ta buge Ecuador inda ta zama ta hudu. Chile, wacce ke matsayi na shida ta sha kashi a hannunBoliviada ci1-0.
Chile, wacce ke bayan Argentina da maki daya, za ta barje gumi da Ecuador kafin ta kammala wasanta da wacce ke matsayi na daya Brazil a watan gobe.
Argentina, wacce sau biyu tana lashe gasar sannan ita ce ta biyu a shekarar 2014, na da maki daidai da na Peru, wacce za su fafata nan gaba, kafin su gwabza da Ecuador.
Bbcahausa
Add Comment