hahararren mawakin fina-finan Hausa nan, Nura M Inuwa, ya bayyana yadda ya samu kwarin gwiwa bayan da aka watsa masa acid.
Nura ya ce abin da ya same shin ya kara masa son jama’a ne, maimakon gudun su.
Ina yaro lokacin inda kuricuya,kawai na tsinci kaina ina waka a baya in an bata min rai nakanyi waka idan an faranta min ma haka,nakan yi waka.
Tambay:A matsayin me ka dauki waka ?
Nura: Na dauketa matsayin Saana ,tanai min amfani wajen tura sakonnin gyara ga Alumma,fadakarwa da kuma nushadantawa da dai
Tambaya: Shin wane ya doraka a hanyar waka?
Nura:Muazzam ne ya fara dorani akan harkan waka sai ya rubuta wakar ya bani sannan ya bani salon kida to bayan ya bani nima na karbeta sai naje na ciccire wasu maganganu da nake ganin sun min tsufa acikin wakar,na gyarata nayi wakar itace wakar salon kida .
Tambaya: Me yasa kake ganin mutane sun gamsu da wakokinka ?
Nura: Nayadda da Allah zai yimin kuma yayi min shi ya cusawa mutane kaunar wakokina a zukatan su kuma suke son wakokina.
Tambaya: Yaushe aka watsawa Nura M Inuwa Acid a ido?
Nura: Ranar asabar ne kuma suka ce suna son za su koma Abuja kuma shi wanda ya kirani cewa matarsa wadda zai aura ce ta dage sai Nura M Inuwa yayi mata waka, ni kuma kusan duk lokacin da akai min irin wadannan maganganu sai a karyamin zuciyata.
Wannan dalilin yasa suka kirani ,suka yaudareni da sanaata suka watsamin Acid wanda ya zama tambari ko in ce shaidar Nura M Inuwa kenan,idan kaga Nura sai da gilas,idan babu gilas toh ba Nura M Inuwa bane .
Tambaya: Wana tasiri hakan yayi wajen kawo koma bayan ko ci gaba a rayuwarka ?
Nura: Na sami kwarin gwiwar abin da nake yi , sannan ya samin kaunar mutane dan da yayi tasiri sai in dinga gudun mutane ,nan ma zai zama matsala gare ni,tunda zan samu raguwar masoya, saboda zance ban yadda da kowa ba.