Raayi

Wata Sabuwa: `Yan Najeriya 5 Da Ke Ikirarin Sun Mutu, Sun Shiga Aljannan Sun Dawo

A Najeriya dai addini abu ne mai muhimmaci inda akwai addinai da dama a kasar tare da dariku da dama.

Addinin kirista yana daga cikin addinin da ke da mabiya masu yawa a Najeriya kuma a cikinsa akwai dariku daban-daban masu aikata abubuwan ban mamaki.

Daya daga cikin abubuwan ban mamakin shine batun dawo da rai ga mutanen da suka mutu. Kuma baya ga haka wadanda suka mutun sukan yi ikirarin cewa sun ziyarci aljanna ko wuta.

Wasu daga cikinsu ma na cewa Allah ya karbi rayuwarsu domin ya nuna musu na’imomin da ke aljanna ko azabar da ke wuta.

Bayan an dawo musu da ransu, galibinsu na ikirarin cewa ba su so dawowa ba amma an dawo da su ne domin su isar da muhimman sako a kan abubuwan da suka gani.

Gai dai biyar daga cikin mutanen da suka shahara a kan cewa sun tafi lahira sun ziyarci wuta ko aljanna sannan suka dawo.

1. Abraham Yakubu

Abraham Yakubu da musulmi ne amma daga bisani ya koma addinin Kirista bayan wai ya yi hatsari kuma ya mutu. An ce wai likitoci sun tabbatar da cewa ya mutu.

Sai dai a yayin gawarsa ke kwance, Abraham Yakubu ya ce an tafi da shi wuta da aljanna inda aka nuna masa wasu abubuwa kuma daga bisani aka dawo masa da ransa domin ya fadakar da al’umma.

A 2016, Abraham Yakubu ya shahara a tsakanin Kiristoci. Duk da cewa kafin shi wasu mutane sunyi ikirarin sun mutu sun dawo amma kasancewar shi musulmi ne da farko kafin ya zama kirista ya sanya mutane da dama razana idan sun ji labarinsa. Bayan wani dan lokaci, labarinsa ya lafa.

2. Shotunde Kayode

A ‘yan kwanakin nan, wani fasto a ‘Uncommon Favour Evangelical Ministry da ke Ibadan a jihar Oyo ya bayyana yadda ya tafi aljanna kuma ya dawo.

Mutumin mai suna Shotunde Kayode ya ce bai san komi game da addini ba amma ya yi hatsarin mota da wasu mutane 17.

An ajiye gawarsa a asibiti tsawon kwanaki 3 domin ba a san iyalansa ba.

A cikin kwanaki ukun ne ya ce an tafi da shi aljannan. Ya ce daga nan ne Ubangiji

#Mikiya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement