Labarai

Wata Sabuwa ‘Yan Film Na Tururuwar Ziyarar Dan Sanda Abba Kyari

-Dan wasan kwaikwayo Zaharaddeen Sani ya ziyarci Abba Kyari

– Abba Kyari ne Gwarzon Jami’in Dan Sandan da ya damke Evans

– ‘Yan wasa dai na ta kai masa ziyara na musamman kwannan nan

Wani fitaccen Dan wasan kwaikwayon Hausa watau Zaharaddeen Sani ya ziyarci babban Jami’in Dan Sandan nan Abba Kyari har Ofishin sa.

Abba Kyari ya bayyana wannan ne a shafin sa na Facebook kamar yadda mu ka samu labari ba dadewa ba. Babban Dan wasan ya taka ne har zuwa Ofishin rikakken Dan Sandar. Ko kwanakin baya dai Baba Ari ya kai masa ziyara.

Dan wasan ya saba fitowa cikin fim a matsayin yaron banza. Shi kuwa Abba Kyari kwanaki yayi nasarar damke hatsabibin mai garkuwa da jama’ar nan watau Evans bayan an dade ana neman sa ruwa a hallo

Kwanan nan ne kuma Sufeta Janar na ‘Yan Sanda Ibrahim Idris ya sallami wasu manyan Ma’aikata 3 daga aiki a Jihar Legas bayan an kama su da laifi dabam-dabam.