Labarai

WATA SABUWA: A Saki Malam Ko A Koma London, Yanzu – inji yan Shi'a

Daga Shafin Hausa Time
Mabiya Shi’a a Najeriya, sun gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoransu dake tsare wato Malam Ibrahim Elzakzaky, da matarsa a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Masu zanga-zangar sun yi jerin gwano har zuwa opishin hukumar kare hakin bil’adama ta Human Rights Commission, dake garin Yola, inda suka samu tarba daga jami’an hukumar.
 
A yayin wannan zanga-zangar lumana, hukumar kare hakin bil adaman ta Najeriya.
Human Rights Commission.
Ta sha alwashin tilastawa gwamnatin Najeriya, har sai ta saki jagoran na yan Shi’a dake tsare tare da matarsa.
Wasu daga cikin matasan da suka gudanar da zanga-zangar lumanar, dai sun rika furta kalaman hannunka mai sanda ga mahukuntan na Abuja, inda wasu suka rika cewa.
A saki malam ko yanzu a koma London da zama, ba tare da an shirya ba.