WATA SABUWA | Babu kiristan zai ɗauki makami yaje ya kashe ƴan uwansa mutane, Martanin ƙungiyar CAN a gun Gwamna zulum

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga El-farouq jakada

A wasu rohoton damu kasamu ƙungiyar kiristocin ta Nijeriya (CAN) ta ƙalubalanci Gwamna zulum kan batunsa, cewa Acikin ƴan ƙungiyar Boko haram akwai kiristan a ciki.

Wannan Bayanin ya fito daga bakin Sakataren ƙungiyar na kasa, Wato Joseph Daramola, a yayin zantawar sa da jaridar Punch.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 693

Idan zamu tuna Gwamna zulum yace a Bayanin sa “Ni dan jahar Borno ne, tabbas akwai ƴayanmu dayawa a wannan ƙungiyar, Amma tabbas akwai masu tallafawa musu, sannan acikin Boko haram Akwai fararen fata da mutanen Asia, Sannan da musulmin gami da kirista”.

Joseph yayin ƙalubalanci da yake wa Gwamnan yace idan har yanaso sun amince da wannan zance to ya kawo shaida koda ta hoton ko kuma Hoton mai motsi dake nuna kiristan a cikin wannan ƙungiyar ta boko haram.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: