Labarai

Wata Mata Ta Gwada Kaifin Hakoranta Kan Makwabciyarta

Wata mata ta gwada kaifin hakoranta akan hannun makwabciyarta yayin da fada ya kaure a tsakanin su.

Lamarin dai ya faru ne a Unguwar Kurna, bayan makaranta cikin birnin Kano.

 

Matan dai guda biyu suna makwabtaka da junan su kowa gidan ta daban, kuma dalilin rigimar ta su akan ‘ya‘ya ne inda har ta kai sun kaure da fada yayinda daya ta ciji daya a hannu har ta kwashe mata fata kuma ba a ga inda fatar ta yi ba.

Maganar dai yanzu tana gaban ’yan sanda kuma da zarar an gama bincike za a tura su kotu kamar yadda ita wadda aka ciza ta nema.