Labarai

Wata Mata Mai Zaman Kanta Ta Sayar Da Danta Dan Wata Hudu Akan ₦300,000

Dubun wata Mata ta cika yayinda Yansanda suka kamata ta saida Dan cikinta a Jihar Katsina, Mai Magana da yawun Rundunar Yansandan Jihar Katsina SP Isah Gambo shine ya bayyana hakan ga mamema labarai a shelkwatar Yansanda dake jihar ta Katsina.

Matar mai suna Zainab Adamu ‘yar asalin jihar Adamawa mazauniyar Kofar Kaura da ke Katsina ta hada baki fa kawarta Ruth Kenneth inda suka sayar wa wata Chidinma Omehyar shekaru 43 daga jihar Anambra danta akan Naira 300,000.

‘Yansanda sun samu kudi Naira 165,000 a jikin Zainab inda aka kuma samu Naira 85,000 a jikin Ruth.

Zuma Times Hausa ta samu labarin cewa har yanzun ana rike da wadanda ake tuhuma yayin da bincike na gudana.

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: