Labarai

Wata Kotu A Amurka Tabawa FBI Damar Su Kamo Abba Kyari

Shahrarren mai damfara a yanar gizo, Abbas Ramoni, wanda aka fi sani da Huspuppi, ya bayyana cewa hazikin dan sanda, DCP Abba Kyari, na cikin wadanda ya baiwa kudin cin hanci. Hakan na kunshe ne a cikin wasu takardu da wata kotun gwamnatin Amurka ta fitar.

Huspupi
Huspupi

Bayan shekara da shekaru yana damfarar jama’a, an damke Hushpuppi a Dubai kuma aka garzaya da shi Amurka. Jami’an kotu a Amurka sun ce yayin gudanar da bincike, Hushpuppi ya bayyana cewa ya baiwa Abba Kyari kudin cin hanci domin ya tayashi kulle wani dan adawarsa dake Najeriya kan harkallar damfarar wasu yan kasar Qatar $1.1 million.

A cewar jawabin da ma’aikatar Shari’ar Amurka ta saki, Huspuppi ya bukaci Abba Kayri ya kulle masa Kelly Chibuzor.

Shahararren ‘Dan 419 a Duniya, Hushpuppi ya amsa laifinsa a kotu, zai tafi gidan yari A binciken da akayi, an gano Vincent ya tuntubi wanda ake shirin damfara a Qatar cewa damfararsa Hushpuppi zai yi. Kawai sai Hushpuppi ya fusata ya tuntubi Kyari da ya daure masa Vincent, cewar binciken. An nakalto Hushpuppi da cewa bayan damke masa Vincent da akayi, Abba Kyari ya turo hotunan yadda suka daureshi tare da lambar asusun bankinsa domin a tura masa kudin aikin.

Hakika wanna makirci ne aka kullowa Abba, domin ganin an ci mutuncin sa an kore shi daga aiki. Tabbas wannan wasu makiyan Najeriya ne da basu bukatar ganin an kawo karshen ‘yan ta’adda suka shirya wannan makirci.

Ya Allah ka yi wa Abba Kyara kariya da kariyar ka.

Ya Allah ka bayyana gaskiyar lamari akan wannan makirci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: