JARIDAR DIMOKURADIYYA: Marigayiyan mai suna Aisha Abdul-Ganiyu daliba ce a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ‘yar 300 level ta kashe kanta ta hanyar Shan gubar maganin kashe Kwari.
Marigayiyar ta rubuta cikin wata Takarda da aka samu a cikin dakin ta dake gidan su a Unguwar Samaru Zariya, cewar ta gaji da rayuwar Duniya shine dalilin kashe kanta, kuma tace kada a Zargi kowa, sannan tayi wasiyar a Gaggauta binne ta gawar ta kada a bata lokaci.
Sannan ta bayyana cewar tana da Kudi Naira Dubu 12 a asusun bankin ta, inda ta bukaci ayi mata sadaka da su, domin neman gafarar ubangiji.
Me za ku ce jama’a?
Jaridar Dimokuradiyya 27/12/2018.