Labarai

Wasu Yan Uwan Ganduje sun koma Akidar Kwankwasiyya

Wasu ‘Yan Uwan Gwamna Ganduje Sun Koma Akidar Kwankwasiyya

Wasu ‘ya’yan ‘yan uwan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje sun koma akidar Kwankwasiyya, duk da irin rashin fahimtar dake tsakanin tsohon gwamnan na Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da kawun nasu.

 

Hauwa’u Muhammad Ganduje da Sadiya Hassan Umar Ganduje da Maimuna Hassan Umar Ganduje wadanda suke tare da rakiyar wani dan uwansu namiji, sun karbi akidar Kwankwasiyyar ne a gidan tsahon shugaban karamar hukumar Tarauni Mukhtar Umar Yarima.

A cewar ‘ya’yan na Gwamna Ganduje, sun shiga akidar ta Kwankasiyya ne kasancewar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na kowane, kuma yana da kaunar mutane tare da karrama su. Don haka ne suka ga ya dace su shiga sahun masoyansa.

 

Rariya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.