Labarai

Wasu Tsirarun Masu Kudin Nijeriya Ne Suka Jefa Kasar Halin Da Take Ciki, Cewar Shugaba Buhari

Daga Comr Abba Sani Pantami

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai wasu yan tsirarun masu arziki da karfin Iko a kasar nan da sune suka yi sanadiyyar fadawa da kasar ta yi halin da muka tsinci kan mu.

Buhari ya ce ya na rokon Allah ya bayyana wa gwamnati su, sai sun gwammace kida da karatu.

Wannan sakon ya na kunshe ne cikin jawabin da yayi wa Dattawan jihohin Barno da Yobe da suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa.

”Ina tabbatar muku da cewa za mu gano wadannan mutane da ke amfani da karfin arziki da dama da suke da shi wajen jefa kasar nan cikin halin da ta ke ciki, su sani ba za su sha da dadi ba idan muka gano su. Ina matukar juyayin abubuwan da kuke gama da su kamar yadda ake fadi tashi sauran sassan kasar nan.

”Muna sane da matsalolin da jihohin ku ke fama da su na rashin ababen more rayuwa.

Za mu maida hankali wajen tabbatar da yara sun koma makaranta, wanda shine ya fi dacewa yanzu.

Duk yaron da bai samu ilimi ba, rayuwar sa na cikin hadarin gaske.

Cikin tawagar da suka ziyarci Buhari, akwa gwamna Babagana Zulum wanda a jawabin sa ya jinjina wa Buhar bisa kokarin da yake yi na kawo karshen Boko Haram a yankin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: