Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da takwarorinsa na jihohin Kano, Jigawa, Osun, Ebonyi, Delta, Kebbi, Zamfara, Katsina, Sokoto da Kaduna sun gana da wani kamfanin noma na kasar China a ‘CAMALO’ a ofishin ministan noma Cif Audu Ogbeh.
Makasudin ganawar wacce aka yi tsakanin Gwamnonin da kamfanin dai shi ne kulla hadin gwuiwa domin samar da hatsi da rogo da alkama a jihohin.
Daraktan yada labarai da sadarwa na fadar Gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakasai ya ce za a cigaba da irin wannan ganawar tsakanin Gwamnonin da kamfanin har sai an cimma nasarar kullawa da aiwatar da yarjejeniyar,
Shirin dai zai taimaka wajen cimma muradin Gwamnati tarayya na rage dogaro da man fetur wajen samun kudaden shiga zuwa komawa fannin noma da kiwo.
Add Comment