Wanne Hali Ilimin Marayu Yake Shiga?

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wanne Hali Ilimin Marayu Yake Shiga?

Allah Swt.Shine Me Kaddara Komai, a Duk Sanda Yaso, Allah Ne Yakaddara Wasu Suzama Marayu Kuma, Yayi Bushara, Ta Harshen Manzonsa Saw, Ga Duk Wanda Yataimaki Maraya, a bangaren Tarbiya, ilimi Dakuma Dawainiyar Rayuwa Ta Yau Da Gobe!

Talla

Asof Tayi Dogon Nazari Da Bincike Akan Rayuwar Maraya Musamman a Bangaren ilimin, Sanin Kowa Ne a Wannan Lokacin, Karatu Ta Kowanne Bangare Yana Buqatar Wasu Kudade Na Gudanarwa, Tundaga Matakin Primary Har Zuwa Sikandire, Dakuma Uwa Uba Tertiary Education Wato ilimin Gaba Da Sikandire!.

Dan’uwa Nasan Akwai Maraya a Unguwar Ku ko Garinku Kataba bibiyar Halin Da Yake Ciki?

Abun Ze Sanya ka Kuka Da Zubda Hawaye Matuka, Asof Tayi Ta Cin Karo Da irin Wannan Matsalolin, Hakika Adadin Yaran Dabasa Zuwa Makaranta, Sbd Talauci Ko Maraici Kullum Kara Yawa Yake,

Abun Takaici Daban Haushi, Yanda ilimin Primary Yake Gagarar Wasu Marayu, Duk Da Cewa ilimin Primary Abunda Ake Buqata Bewuce Kudin Uniform Da Littafin Rubutu Ba,

Sai Kuma Dan Abun Da baza’a Rasa Ba, Na #10 Daza’a Bawa Yaro Yatafi,

aji, Amma Asof Tagano Yara Dayawa Marayu Wanda Uniform Yahanasu Zuwa Makaranta, Wannan Matsalar, Tashafi Duk Wanda Yakaranta Wannan Rubutun, Yakai Dan Uwa, Meyasa Baka Taba Tunanin Kai Yaro Daya Makarantar Primary Ba? a Lokacin Da iyayen Sa, Suka Gaza, Kokuma Suka Rasu.

a Kalla Abun da Ake buqata be Wuce Dubu Daya ba, Karka Manta, a Dubu Daya Zaka Ceci Rayuwar Sa, da Ya iyalin Sa, Dama Al’ummar Dayake Cikin Ta.

Idan Muka Gangara Matakin Sikandire Kuwa Dan Uwa Abun Ba’a Cewa komai, Domin Kuwa Matasa Dayawa Sun kasa Daukar Nauyin Karatun Su a Sikandire Sbd Sune Suke ciyar Da kansu Kuma, Suke Yiwa kansu komai, a Lokacin idan Suka je Makarantar Abun da Zasuyi Rayuwar Ma Ze Gagare Su, Asof Taci Karo Da Wani Dalibin karamar Sikandire Ta kwana Mun Boye Sunan Sa, Amma Ya Shaida Mana Cewa Shekarar Sa, Goma Sha biyar Mahaifin Sa Yarasu, Daga Nan Yarasa Me Daukar Nauyin karatun Sa, Na Junior Secondary School, Yaron Yayi Ta Amfani Da Lokacin Hutun Karshen Zango Wajen Nemawa Kansa kudin Dazai koma Makaranta,

Asof Ta Tambaye Shi Shin Abunda Kake Samu yana isar ka har Zuwa Lokacin Hutu? Amsar itace A’a

“Daga Nakoma Makaranta Bana Siyan Sabulun Wanki Dana Wanka Abokaina Nakeyiwa Wanki Subani Guntun Sabulu, Dashi Zanyi Wanki Na nayi Wanka, idan Abincina Yakare Haka Nake Yiwa Abokaina Diban Ruwa da Girki Dan Muci Abincin Tare ” injishi.

Wannan Yasanya Ni Zubda Hawaye Sosai.

Bayan Haka Asof Takara Ganawa da Wani Dalibin Sikandiren jeka Kadawo, Wanda Yashaida Mana Cewa;

“Nine Namaida Kaina Makaranta Bayan Nafahimci Mahaifiyata Bata Samun Abincin Rana Sai Nake Zuwa Talla Domin in Nemo Mata Abinci Dani Kaina to a Karshe Nakoma Sinkandiren Yamma, Bayan Nadawo Daga Talla sai Intafi Makarantar “.

Idan Kuwa Kakoma Ilimin Gaba Da Sikandire Abun Ba’a Cewa komai Domin adadin Daliban Da Basa Zuwa Makaranta Sbd Baza Su iya Daukar Nauyin kansu a Jami’a ko Diploma ba, Babu iyaka, Asof Tayi Ta Cin Karo Dasu Sosai wasu Basu da kudin jamb Wasu Kuwa basu da kudin Registration na Makarantar, Wani Abu Daya Saka Ni Zubda Hawaye,

Wani Dalibi daya Samu Admission a Jami’a Yayanke Shawarar Hakura Bayan yayi Registration Din Farko dalibin Yashaida Mana Cewa;

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 6

” Ni Sana’ar Hannu Nakeyi Nayi jamb Nasamu Admission Amma Matsala Ta Yanzu bazan iya Daukar Nauyin karatun Ba, Sbd Abaya Kullum Ina Samun 500 Awajen Aikina, Amma idan Naje Makaranta ko sisi Bana Samu Kuma Wlh Sai de Nasha Ruwa Domin Babu Abinci Tunda bani da kudin Siya ” injishi.

a Lokacin Da yake Magana da Asof Yafada Mun Cewa Yahaqura kawai zai Dena Zuwa.

Haka Asof Taci gaba da Gano Dalibai Masu Hazaka, Sosai Wanda Basu da kudin Yin jamb ko Zana Jarrabawar Neco ko Waec.

a 2017 Wani Dalibin Ajin Karshe Na Sikandire Ya kauracewa Yin Neco ko Waec, a Lokacin Da Asof Take Tattauna Wa Dashi ya Shaida Mana Cewa Babu kudin Ne

“Inada Dubu Goma Sha Uku Amma shine Capital Din Danake Juyawa idan Nabiya kudin Neco Babu inda Zansamu Abunda Zanci Tocila Nake saidawa Nayi Hasashen Zan iya Tara Wani kudin Nan da wata shekara ” Inji Dalibin.

Wani Dalibi Kuwa, Fashewa Yayi da kuka a Lokacin Da Yaga Dabbobin Sa, Daya Baro a Kauyen Su, Sunkare Kuma a Lokacin Yana aji Biyu Na FCE, koda Asof ta Bincika Ta Gano Cewa Dalibin Yayi Hasashen Ze iya Barin Makarantar Ne, Duk da Cewa yayi shekara Biyu Tunda Dabobi Sunkare.

Asof Takara Cin Karo Da Wani Dalibi a Wata FCE Daya Bar Makarantar Ana Tsakiyar Jarrabawa, Wannan Kuwa Dakai Na Neme Shi Akace Mun Yakoma Gida Sbd Sama da Sati Bashi da Abinci a Makarantar, Ban San Lokacin Da Hawaye yazubo Mun ba!.

Asof Bata Da Wani Kudi a Asusun Ta, Datake iya Taimakon Dalibai, Hanya Daya kawai Asof Take iya bi Domin Taimaka Musu, Asof Tana Amfani Da, Letter Head Din Ta, wajen Rubutawa Wasu kungiyoyi Wasiqa Kokuma Wasu Masha Huran Mutane, Domin Su Tallafawa Dalibin,

Asof Tana Rubuta komai a Wasiqar Kuma Asof bata buqatar, Abawa Dalibin kudin a Hannu ko Abawa Asof A’a Asof Tana Buqatar kayi Amfani Da Asusun Bankin ka wajen Biyawa Dalibin Kokuma kaje Makarantar Da Kanka, Asof Taci Nasarar Maida Dalibai Dayawa Makaranta ta Wannan Hanyar, koda Yake Abun Da Yawa.

Wata Daliba da Asof Tasamawa Admission Dalibar ta Shaida Mana Cewa Tagano baza ta iya Daukar Nauyin karatun ba Duk da Cewa Tana da kudin Registration Amma Kullum Zata Kashe Kudi Naira 300 Na mota zuwa Makaranta Wanda Tasan Babu inda Zata Samu Wanda Daga Karshe Asof, Tayi kokarin Wani Bawan Allah Yayi Alkawarin bata 300 a Kullum, har Tsawon shekara Uku, Nan aka Lissafa Na Semester Daya Yabiya.

Hakama Asof Tana Da Hadin Gwiwa Da Wata Kungiya Ta Marayu Wacce Atakaice Ake Cemata “Olepemcos” Kungiyar Tana Daukan Nauyin karatun Yara Yan Primary Sama Da Dari Biyu a Duk Shekara.

Asof Tana Amfani Da Wannan Damar, Wajen Kiran Al’umma Su Taimaka, Basai Mai Kudi ko Dan Siyasa Ba, A’a kowa Yana da Damar Da ze iya Taimakawa Dai Dai Karfin Sa.

Yakamata Mu Fahimci Cewa Masu Taimakon Mu Sunyi Karanci, Sbd Haka Dole Mu Hada Kanmu Mu Taimaki Kan Da Kanmu.

Asof Bazata iya Lissafa ko Ambata muku irin Matsalar Datake Damun Al’ummar Nan Tamu a bangaren Karatu ba Saide Kawai Abada Misali Atakaice!.

Muna Fatan kowanne Yanki ko Wanne Gari Zasu Kafa Kungiyar Taimakon Marayu da kuma Marasa Galihu a bangarori da dama Musamman Uwa Uba bangaren ilimin Mu, Wanda a Yanzu Shine Jigon Rayuwar Mu.

Mungode!!!

Asof/24/11/2018

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: