Kiwon lafiya

Wanne Amfani Alkama Ta Ke Da Shi?

Bincikr ya nuna cewar amfani da Alkama abin yana da matukar muhimmanci saboda tanasamar da wata kariya daga wasu cututtuka masu matukar tasanani, sai kuma rage yiyuwar mutuwar jarirai da kuma kananan yara. Abinci wanda ya kunshi binciken ya nuna shi ma yana rage yiyuwar kamuwa da cututtukan da suke da alaka da zuciya da kuma hanyoyin jini, yana kuma taimakawa wajen daidaituwar nauyin mutum.

Masana ilmin kimiyya a jami’ar gabashin Finland a Kuopio suna samun nasara wajen binciken da suke saboda gano amfanin kwayoyin halitta na Alkama da kuma gudunmawar da hakan ke bada waakan taimakawa lafiyar jikin Dan adam. “ Wholegrains ko kuma Alkama tana daga cikin kayayyakin abinci masu nagarta da kuma inganci, alal misali idan mutum yana cin wholegrains da yawa, yana samun kariya daga cutar sikari ta 2 da kuma Cardiobascukar diseases, kamar dai yadda babban mai bincike Dokta Kati Hanhineba ya bayyana. “ Har zuwa yanzun ba a kai ga gane yadda kwayar halitta wadda a dalilinta Alkama tana yi mana amfani a jikinmu”. Binciken da ba a dade da yi bay a duba amfanin ita Alkama akan wata halittar mice da kuma mutun dan adam, bayan nan kuma sabon bayanin da aka samo an wallafa shi bada dadewa ba, a mujallar da ta kunshi bincike akan al’amarin daya shafi abinci.

Bayan da mutanen da aka zazzabo sun ci abincin daya shafi wholegrains har zuwa makonni goma sha biyu, sai kuma su masu binciken suka yi wani nazari akan metabolomics, wanda kuma shi wani nazari ne wanda ake gane yadda metabolites suke, wadanda su wasu kananan sinadarai ne wadanda lokacin da ake sa ran ganin wani sakamako akan hanyoyin da ake bi na metabolic.

Su masu binciken su babban abinda yafi burgesu shine sinadarin betaine wanda shima yana daga cikin wasu kwayoyin halitta, wadanda suma suna daga cikin ayyukan da suka shafi jikin dan adam. Alkama wani nau’i ne ne kayan abinci wanda ake samu sinadarin betaine, bayan nan kuma su masu binciken, sun ci wani abincin rana wanda zai taimaka masu wajen bayyana yadda amfanin ita Alkama ga lafiyar jikin dan adam.

Kamar dai yadda aka yi tsammani binciken da suka yi sai ya nuna masu an samu karuwar sinadarin betaine, wannan kuwa ya kasance haka ne saboda samun halin cin abincin daya kunshi whole grain har zuwa makonni goma sha biyu.

Wannan ya bunkasa mizanin shi betaine a dukkanin abubuwan biyu da aka yi bincike akan su. Kamar dai yadda Dokta Hanhineba ya bayyana “ Wannan shi ne lokaci na farko yawancin su wadannan sinadaran aka fara ganin su a jikin mutum”.

Masu binciken sun gano wasu abubuwa wadanda suna da bambanci tsakanin yawan mizaninsinadaran betaine, da kuma kyautatuwar sinadarin glucose metabolism, wadansu daga cikin su wadannan sinadaran ko wanne sai a lura kamar yafi dayan. “Sinadarin Pipecolic acid betaine alal misali shi yana karuwa, don haka karuwar mizanin pipecolic acid betaine, bayan cin abincindaya kunshi whole grains, daga cikin wasu abubuwa wadanda suke dangantaka da mizanin sinadarin glucose “kamar dai yadda Hanhineba ya bayyana.

A wani binciken da aka yi ‘yan tawagar sun sake gwada wasu sinadaran akan wata kwayar halitta a dakin bincike, babban abinda suke bukata shi ne sindaran 5-aminobaleric acid betaine (5 -ABAB) , wanda kuma aka sani cewar yana dauke da wasu sassa masu amfani kamar cardiac tissue.

Sakamakon da aka samoa sanadiyar shi binciken yana iya taimakawa wajen binciken cutar data shafi cardiobascular.

“Sun gano cewar 5- ABAB yana rage cardiomyocytes amfani da sinadarai daga kwayoyin halittar abincincin daya kun shi fat, a matsayin wata hanya ce ta samun kuzari, ta amfani da wata kwayar halitta, daga cikin protein.

Wannan abin murna ne saboda kuwa wasu magungunan cardiac suna ayyuka da suka kasance daya, amma kuma duk da hakan su ‘yan tawagar sun bi a hankali saboda kada su kawo ga sakamakon shi al’amarin kafin a yi wani bincike a wasu dabbobi.

Amma kuma yana da muhimmanci a gane cewar shi binciken ba ya bane kawai akan zagayen wata kwayar halitta.

Gaba daya dai su abubuwan da suka gano sannu a hankali sun kara sani da kuma fahimtar, da kuma yadda amfanin whole grains yake ga lafiyar jikin dan adam.

Hakanan ma sun yi wasu tambayoyi wadanda suke bukatar amsa.

“Nan gaba da akwai bukatar da a yi bincike da kuma nazari sosai akan yadda shi amfani ko kuma akasin shi, su wadannan sababbin kwayoyin halitta zasu samar ma jikin dan adam” kamar dai yadda shi Hanhineba ya yi bayanin shi”.

“Ya kamata mu yi bincike saboda mu gano amfanin yadda shi wani sinadari ko kuma kwayar halitta suke a jikin dan adam.”

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement