Labarai

Wannan Shine Abunda Ke Damun Buhari

WANNAN SHINE ABIN DA KE DAMUN BUHARI – INJI WANI MAI AMFANI DA FACEBOOK

Wani masanin ilmin tsibbu dake amfani da shafin facebook ya bayyana cewa siddabaru da yanka da yan shia suka yi a shekarar da ta wuce shine sanadiyyar mawuyacin halin da shugaba Buhari ke ciki a yanzu.

 

Masanin mai suna Muhammad Muhammad Kofa ya kara da cewa muddin gwamnati bata gyarota da wadanda suka yi asirin ba to karyashi zai yi wuya.

Ya kara da cewa a matsayinsa na masoyin Buhari yayi iya kokarinsa na ganin ya karya sihirin amma abin ya gagareshi.

Ya kara da cewa duk sihirin da aka hada da Qurani, wuta da jini aka binne a rami to yana da matukar wuyar shaani a wurinsu.

Don haka yayi kira da yan shia da su tausayawa halin da shugaban kasa da iyalinsa da yan kasa ke ciki don ganin sun karya wannan sihiri.

Ya kuma shawarci iyalin shugaban kasa dasu gaggauta sasantawa da wadanda sukai wannan aiki don ganin cewa Baba ya sami lafiya.

Daga: Nigerian Dan Arewa

Me zaku ce?