JARIDAR DIMOKURADIYYA:An kaure da cece-kuce, kuma hakan na kushe cikin bayyana raayoyi game da Hoton dake manne da wannan labari da muka wallafa muku, wanda ke nuni da wani Jami’in Soji dake farautar zuciyar Jarumar masanaantar shirya fina finan Hausa Kannywood Nafisa.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilimu Shuaibu Abdullahi, a safiyar yau Jumaa, Zaharaddeen Nasir ya bayyana mana cewar lallai ba kazafi bane shine da kan sa ya wallafa Hotunan tare da Lambar wayar sa, yace yana matukar kaunar Jarumar kuma yana fata zata Amince masa da Aure.
Zaharaddeen Nasir ya bayyanawa Jaridar Dimokuradiyya cewar shi haifaffen Jihar Sokoto ne to amma yanzu haka aiki ya kai shi Benuwe, kuma shi Sojan ruwa ne Navy, yace yana matukar kaunar ta musamman idan yana kallon Hotunan ta.
- Advertisement -
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar yanzu haka dai Al’umma da dama suna yi masa fatan Alkairi, da rokon Allah ya cika masa burin sa.
Zamu yi kokarin jin ta baki ita Jarumar don jin nata bangaren game da batun.