Nasiha

WANI SIRRI YAKAMATA KUSANI

_WANI SIRRI YAKAMATA KUSANI_
*MAHAKURCI mai Karfi ne koda a zahiri karfin bai Nuna bah,Don ko mai Hakuri baya taba tabewa,MAI Hakuri Yana tare da ALLAH.*

*MAI KYAUTA ba sakarai bane,mutane na daukan mai sakin hannu wajen kyauta a matsayin sakarai,kar mai zaton yazama mai sunan?*

*TAUSAYI alamar imani ne,mai tausayi baya zama azalumi.*

*YIN AFUWA sai Wanda ya isa,idan kafi karfin Abu sai dai ka bashi baya ba dai kace zaka rama bah.*

*SANIN DARAJAR mutane sai Dan gidan dattako,duk mai wulakanta mutane arzikin ko girman rana tsaka ya same shi.*

*GULMA ALAMAR TSORO NE idan ba tsoro bah tun kareshi kafadi Mashi laifin shi don ya gyara.*

*HA’INCI ALAMAR KWADAYI NE duk abinda aka samu ta hanya ha’inci babu Albarka.*

*HASSADA ALAMAR BAKIN HALINE abinda bah kai ka bashi bah,don mi zaka yi Bakin ciki?Roki ALLAH kaima ya baka Rabon kah.*

*GAGGAWA Halin shedan ne,baka San sanda kazo ba,baka San sarda zaka koma bah,kayi hakuri Tunfil Azal ALLAH ya Riga ya shiryama rayuwar ka,da lokacin Abu yazo zai zo ba sai ka taddashi bah.bazaka mutu ba sai kacinye rabon kah.*

*FADIN RAI ALAMAR GIRMAN KAI,mutumin da bai iya yima kanshi maganin Rabin lalurar shi,fadin ran na minene?*

*MAI SURUTU ALAMAR MAKARYACI NE,dole sai kabada labarin? Yi shiru mana bakinka ya huta.*

*CIN AMANA HALIN MUTUMIN BANZA,shi kanshi bai yarda da kanshi bah ya za’ayi a rike amanar wani?*

Rubutawa

Abu Ammar

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.