Wani sashe na mabiya darikar shi’a reshen jahar Kano sun gudanar da taron addu’a ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Addu’o’in nasu dai sun mayarda hankali ne akan samun lafiyar shugaban da kuma zaman lafiyar kasa.
An gudanar da taron ne a unguwar Dorayi karkashin jagorancin wani babban Malaminsu mai suna Muhammad Nur.
Baya ga haka, akwai rade radin cewa mabiya shi’an za su fito gangamin nuna goyon baya ga gwamnatin Buhari a cikin wannan makon.


Add Comment