Labarai

Wani Mutum Ya Shirya Zuwa Ganin Buhari A Keke

Daga Sani Maikasset Malammadori.

Wani bawan Allah dan jam’iyyar APC ya shirya kayan sa tsaf ya daura a bayan kekensa ya kama hanyar zuwa birnin London domin ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

Mutumin Wanda ya baiyana cewar zai je birnin London domin dubo jikin shugaban kasar,
Yace tunda har shugaban yana samun damar ganawa da mutane, to shima ya kudiri aniyar ganin shugaban koda ana ha maza ha mata.

Tuni dai mutumin ya kama hanyar birnin landan bayan yayi sallama da ‘yan uwansa da iyalansa.