‘Yan sanda na zargin wani mutum da kashe matarsa a cikin jirgin ruwa a jihar Alaska ta Amurka saboda “ta ki daina yi masa dariya”.
Ana zargin Kenneth Manzanares da laifin kisan matarsa mai shekara 39, wacce aka gano gawarta an yi mata raunuka da dama a kanta a cikin jirgin ruwan.
An tsare shi bayan jami’an tsaro sun ga jini a hannu da tufafinsa, kamar yadda wasu takardun kotu suka nuna.
Lauyan da kotu ta nada domin ya kare Mista Manzanares bai ce komai a kan batun ba.
Kafofin watsa labaran Amurka sun ce sunan matar Kristy Manzanares, daga jihar Utah.
Wani shaida da ya shiga jirgin ruwan tare da ma’auratan ya ce ya ga lokacin da mijin ke jan gawar matarsa a bayan dakinsu na jirgin.
Da aka tambayi Mista Manzanares kan hakikanin abin da ya faru, ya yi zargin cewa: “Ta ki daina yi min dariya.”
Daga bisani lokacin da jami’an hukumar FBI suka yi bincike a jirgin, mutumin ya shaida musu cewa: “Tawa ta kare.”
Lamarin ya auku ne a daren Talata lokacin da jirgin ruwan na Emerald Princess, na kamfanin Princess Cruises ke tafiya.
A ranar Lahadi ne jirgin ya tashi daga Seattle inda zai yi tafiyar mako guda da fasinja 3,400.
Add Comment