A wani lamari da ke nuna irin yadda wasu mayakan kungiyar Boko Haram da ke yin waswasin dorewar kungiyar da kuma halaccinta, wani dogarin tsaron wani na hannun damar, Abubakar Shekau, ya watsar da kungiyar tare da yin wasu bayanai da ke tona asirin kungiyar.
Cikin cigaban gane gaskiya da wasu mayakan Boko Haram ke yi har suna barin kungiyar, wani daga cikinsu da ya tuba kamar sauran, ya mika kansa ga jami’an tsaro.
Inda ya bayyana cewa, ”Suna na Bara Umara shekaru na 27, kuma na fito daga cikin dajin Sambisa ne, ni dan Banki ne na shiga cikin wannan kungiyar ta Boko Haram ne a lokacin da kungiyar ta shiga cikin garin Banki.
”A lokacin inada wani aboki na mai suna, Abu Mujahid, da ya yaudare ni ya shigar da ni cikin wannan kungiya ta Boko Haram, inda ya ce mani ‘yan Najeriya arna ne kuma sojinta ma arna ne, saboda haka in zo mu je bangaren Shekau saboda shi ne Musulmin na gaskiya, mu je mu yi yaki mu kashe arna marasa Imani”.
”Yayin da na ji tsoro zan tsere, sai ya ce dani da zarar ka ce tserewa za ka yi kashe ka za mu yi kawai saboda ka riga ka san sirinmu”.
A dajin Sambisa sunan da na ke anfani da shi, Abu Mustapha, kuma ni dogarin tsaron Gaidam ne, wanda ke kusa da Abubakar Shekau, kuma na je yake-yake har sau shida a Bama da Wulari da Bita da kuma gefen Tafkin Chadi, idan kuma soji su ka shiga dajin Sambisa muna kai musu farmaki.
Add Comment