Shugabar Karamar Hukumar Konshisha, Misis Justina Ubebe, a jihar Benuwai ta tabbatar kashe waya yarinya da mahaifinta ya yi da nufin yin tsafi a kauyen Tse-Agberagba da ke garin.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya tabbatar da aukuwar lamarin ta hanyar tattaunawa ta wayar tarho yau Alhamis a Makurdi babban birnin jihar. Inda Ubebe ta bayyana lamarin a matsayin abin al’ajabi.
- Advertisement -
Lamarin ya faru ne a daren jiya Laraba kuma an sanarwa ofishin ‘yan sanda.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar ‘yan sandan jihar ASP Moses Yamu ya ce, a yanzu haka an kama bokan da ya umarci a aikata kisan ana ci gaba da bincike.