Labarai

Wani Alhaji Ya Tako Tun Daga Kasar Sa Har Makkah tafiyar kilo mita 9000

Wani matashi dan kasar Indonesiya mai suna Khamin Setiawan ya isa garin Makkah, kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana, kamar yadda shafin Ilmfeed ta ruwaito.

 

Tun a ranar 28 ga watan Agusta na shekarar 2016, hakan ke nufin Khamin ya shafe shekara daya cif cif yana shafa sayyada da nufin zuwa aikin Hajj, sa’anann ya hada da yin azumin nafila yayin dayake tafiyar.

Majiyar Ya ruwaito Khamin ya bayyana cewar ya ratsa kasashen da suka hada da Malaysia, Thailand, Myannar, India, Pakistan, Oman, hadaddiyar daular larabawa da kuma Saudiyya, inda ya kara da cewa yawancin tafiye tafiyen nasa yayi shi da dare ne.

Khamin yace bai taba yin bara ba yayin dayake balaguronsa, amma yace ya hadu da jama’a da dama da suka taimaka masa da abinci da sauran kayayyakin bukatunsa.

Dayake bayanin makasudin sa na gudanar da wannan tafiyar, Khamim yace yayi wannan tattaki ne don Allah da nufin neman yardarm Allah.

 

Souce In Mikiya