Labarai

Wane Ne Magajin Shugaban Kasa Buhari?

Wane Ne Magajin Buhari?

Daga Kabir Muhd Mataimaki

Duk Arewa Mutum Daya Kadai Zai Iya Kwashe Kuri’u Tare Da Soyayyar Mutane Kashi Tamanin Cikin Dari. Matukar Ka Cire Wannan Dan Batalikin, To Babu Wani Mahalukin Da Zai Iya Samun Haka Daga Arewa Duk Daukaka, Mulki, Ko Kuma Arzikin Shi.

To Wannan Mutumi Dai Ba Wani Ba Ne, ILLah Baba Buhari, Wato Shugaban Kasar Da Ke Mulki A Yanzu.

 

Allah Ya Azurta Buhari Da Kwarjini Tare Da Farin Jinin Mutane, Musamman Talakawa.

Buhari Ya Na Da Kima, Mutunci, Daraja, Da Martaba A Idon Duniya Kasancewarsa Adali, Kuma Jagora Nagari.

Duk Yadda Mutum Ya Kai Ga Kin Buhari, To Bai Isa Ya Kira Shi Barawo Ko Azzalumi Ba, Wanda Ya Saka Duniya A Gaba. Sai Dai Mutum Ya Ki Shi Don Wani Ra’ayi Na Shi Na Daban.

To Shin Abin Tambaya Anan Shine, Matukar Baba Buhari Ba Zai Sake Yin Takarar Shugabancin Kasarnan Ba, Wa Mu Ke Ganin Zai Iya Maye Gurbin Shi Daga Arewa, Kuma Wanda Talakawa Za Su Yi Na’am Da Shi?

 

Daga Jaridar Rariya