Labarai

Wandon lauya ya kama wuta ana shari’ah kan ta da gobara

An san sigari mai amfani da lantarki da kama wuta haka kwatsam.
Wandon lauyan mai kare wani mutum da ake ƙara, ya kama da wuta a gaban kotun Florida ana tsaka da shari’ar ta da gobara.
Shaidu sun ce aljihun Stephen Gutierrez ya fara bal-bal da hayaƙi lokacin da ya tsaya gaban kotu, don yi wa masu taya alƙali yanke hukunci jawabi a ranar Laraba.
Daga nan sai lauyan ya fita a guje, kuma ya dawo kotun da ƙonannen aljihu ba tare da jin rauni ba, inda ya zargi baturin taba sigarinsa ta lantarki, a cewar Miami Herald.
Mr Gutierrez, wanda ke mujadala kan cewa motar mutumin da yake karewa haka kawai take kamawa da wuta, ba wani hatsabibanci ne ya shirya ba.
‘Yan sanda da masu shigar da ƙara sun gudanar da bincike kan lamarin, inda jaridar ta ruwaito cewa har jami’an tsaro sun ƙwace baturan sigarin lantarki da suka toye a matsayin shaida.
Lauyan na wakiltar Claudy Charles, wanda ake tuhuma a kan cinna wa motarsa wuta da gangan.
Daga bisani dai kotun ta samu Claudy Charles da laifin tada gobara.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement