Wani Ba’amurke, Larry Roberts mai kirkira-kirkire wanda ya taimaka aka kirkiri intanet ya mutu yana da shekara 81.
A 1960, ya kasance cikin wani bincike mai suna ARPA wanda aka kawo domin hada na’urori masu kwakwalwa su yi aiki a tare.
Kuma shi ne wanda ya dauki wasu injiniyoyin da suka hada sassa da kuma manhajar da ake bukata domin tsarin yayi aiki.
Tsarin Arpanet ne ya zama wani tubali da aka daura intanet da ake amfani da shi a yanzu.
Dr Roberts tare da Bob Kahn, Vint Cert da Len Kleinrock ne suka hada intanet.
Dr Roberts ya mutu ne a ranar 26 ga watan Disamba sakamakon bugun zuciya da ya same shi kamar yadda iyalinsa suka bayyana.
#bbc hausa