Wanda Ya Dauki Bidiyon Rashawar Ganduje Zai Bayyana A Majalisa

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Daga Shafin CNN Hausa

LABARI DA ƊUMI-ƊUMI: Wanda ya naɗi faifen bidiyon Gwamna Ganduje yana karɓar Rashawa ya amince da bayyana a gaban kwamitin bincike, sai dai ya bada wasu sharuɗai.

Talla

A wata wasiƙa Mai shafi uku da lauyan wanda ya naɗi video mai nuna wani mutum yana baiwa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje OFR na jihar Kano kuɗaɗen da ake tsammanin Rashawa ne, Barista Saidu Muhammad Tudunwada ya baiwa ƴan kwamitin wasu sharuɗɗa guda shidda kafin bayyana a gabansu domin bada shaida akan faifen bidiyon.

Daga cikin sharuɗɗan shidda, akwai sharaɗin dole sai Gwamnan da kansa ya bayyana a gabansu maimakon ya aiko da wakili. Sannan yace yana da buƙatar ace baya da Gwamnan, a samu ɗan jaridar daya fitar da bidiyon watau Jaafar Jaafar, sai kuma shugaban Hukumar Hisba Mal. Aminu Daurawa shima ya kasance a wurin yayin bayyanarsa gaban kwamitin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yaba Wa Gwamna Mai Mala Kan Inganta…

Talla
1 of 661

Daga nan sai ya ƙara da cewa domin tantance sahihancin bidiyon kuwa, ya kamata kwamin ya gayyato masana ƙwararru daga ƙasashen waje ta hanyar hukumomin jakadancin ƙasashensu, sannan kuma a gayyato wakili daga hukumar tsaro ta ciki DSS.

Daga ƙarshe lauyan ya nemi idan an tashi zaman jin ba’asin, yana buƙatar tsaro ga lafiyarsa, sannan kwamitin ya sahalewa wanda zai bada Shedar sakaya fuskarsa gami da sakaya sunan sa domin kariya ga kansa, iyalansa da kuma kasuwancinsa.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: