A zaman majalisar zartarwa ta kasa a yau, Gwamnatin tarayya ta amince ministan sardawar na kasa, Dokta Isa Ali Pantami, da ya gina cibiyar horas da sabuwar fasahar sadarwa ta kasa “national ICT park” a birnin tarayya Abuja, saboda ta zama cibiyar da zata shugabanci dukkan cibiyoyin fasahar sadarwa ta zamani a nijeriya, ya kuma zama wujen horar da ‘yan kasa da samar musu da sanao’i da abun yi.
Wannan amincewar ta samu sahalewa sakamakon wani kudiri da minista isa pantami ya gabatar tunda farko.
Ministan ya yi fatan samar da cibiyar ya zama mai amfani ga dukkan ‘yan nijeriya a duk inda suke.
Daga Suleiman Abba (TBABA)