Labarai

Wai idan har Najeriya ta balle to kudancin Kaduna Biyafara za su bi – Danfulani

– Dakta John Danfulani ya kai ziyara jihar Abia don nuna goyon baya ga shugaban Biyafara da kuma bayyana cewa idan har Najeriya ta balle tabbas Biyafara za su bi.

Shugaban kungiyar kawo cigaba da kare hakkokin zamantakewa, Dakta John Danfulani, ya bayyana cewa al’ummar kudancin Kaduna sai sun fi son tafiya tare da yankin Biyafara idan har Najeriya ta balle.

John yayi wannan bayani ne a lokacin da ya kai wata ziyara jihar Abia don nuna goyon baya ga shugaban mazauna yankin na Biyafara, Nnamdi Kanu.

Yace al’ummar kudancin Kaduna suna da alakoki wadanda su kayi tarayya a kai, don haka muddin Najeriya ta balle to kuwa ba za suyi wata-wata ba Biyafara za su bi.

Yayi korafin cewa mazauna yankin kudancin Kaduna kalilan idan ka hada wadanda suke da al’adu irin na sauran jama’ar arewa kuma yawancin su na bin addinin kirista ne, wanda haka shi yasa gwamnati take nuna mu su wariya da nuna ko oho a kan irin cin kashin da makiyaya su ke musu a yankin.

Danfulani ya kara da cewa. idan har Najeriya ta balle to kuwa ba za su bi arewacin kasar nan ba don tabbas Biyafara za su bi don su ne suke da alakar ta al’adu iri daya da kuma addini, kuma wannan zai sa su hada kai su ma su gina ta su kasar don saboda ya fuskanci mutanen arewa ba su kaunar su don su ba al’adar su ba ce kuma uwa uba ba sa fuskantar gabas don yin sallah.